Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zumuncin Sin da Afirka ba zai taba sauyawa ba
2020-04-23 09:07:22        cri

A ranar Talata 14 ga watan Afrilun shekarar 2020 ne, ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, da jakadan Sin dake Najeriya Dr. Zhou Pingjian, suka kira taron manema labarai tare, inda suka yi karin haske kan gaskiyar abin da ke faruwa kan batun wai cin zarafin 'yan Najeriya wadanda suke birnin Guangzhou yayin da ake kokarin dakile annobar COVID-19, bayan wasu suka yi watsa wasu hotunan bidiyo a kafafen sada zumunta.

A hannu guda, a wani taron manema labarai da aka shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, mai gana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Mr. Zhao Lijian ya bayyana cewa, a kwanakin nan, Sin da kasashen Afirka na tabbatar da tuntubar juna da yin shawarwari yadda ya kamata dangane da halin da 'yan Afirka mazauna lardin Guangdong na kasar ke ciki.

Mr. Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, manufar Sin ta sada zumunta da kasashen Afirka ba ta sauya ba, kuma tana daukar matakai na bai daya kan 'yan gida da kuma baki da ke lardin Guangdong a yayin da ake fuskantar matsanancin hali na shigowar cutar COVID-19 daga ketare. Ya ce, "Da yawa daga cikin gwamnatocin kasashen Afirka da ma jakadunsu a kasar Sin suna ganin cewa, domin kare lafiyar al'ummar Sinawa da ma baki 'yan kasashe daban daban ne ake daukar matakan a lardin Guangdong, don haka ya kamata baki mazauna wurin su ba da hadin kai da goyon baya. Kasashen Afirka na jinjinawa kasar Sin kan yadda take ba da muhimmanci wajen kulawa da su, sun kuma lura da cewa, halin da baki 'yan Afirka ke ciki ya inganta sosai a sassan da abin ya shafa. Baya ga haka, wasu abokanmu na Afirka sun nuna cewa, bisa binciken da aka yi, an tabbatar da cewa, wasu hotunan bidiyon da ke yawo ta yanar gizo an yi musu kwaskwarima, ba ainihin gaskiyar lamarin da ya faru ba ne. Don haka, kamata ya yi Sin da Afirka su yi taka tsantsan a kan wadannan bayanan da ka iya sanya al'umma yi musu bahaguwar fahimta

Gaskiyar batun shi ne, wata mace Basiniya mai shagon sayar da abinci ta kamu da cutar, wannan shagon cin abinci kuwa wuri ne da 'yan Afrika ciki har da 'yan Najeriya suke taruwa domin cin abinci. Saboda haka, gwamnatin birnin ta sanar da rufe wannan shago, tare da killace wadanda suka yi hulda da wannan matar, hakan ya sa duk mutanen da aka killace, babu shakka ba za su iya komawa otel din da suke zaune, ko wuraren kwana da suke ba. Wasu 'yan Najeriya dake cikin kasar sun kalli bidiyon da ya shafi lamarin da aka yada a shafin sada zumunta na Intanet, sa'an nan sun yi gurguwar fahimtar cewa, wai ana nuna bambanci ga 'yan Najeriya, da ma sauran 'yan Afrika a birnin Guangzhou, yayin da ake tsaka da yaki da cutar, har ma suka nuna rashin amincewa da hakan. Saboda zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka, ya sa bangaren Najeriya ya tuntubi ofishin jakadancinmu dake kasar Sin, da karamin ofishin jakadancinmu dake birnin Guangzhou da mukaddashin karamin jakadanmu a Guanghou, inda suka tabbatar da cewa, abubuwan dake cikin wannan murya da wani dan kasuwar Najeriya mazaunin Guangzhou ya aike gaskiya ne.

Bangaren Sin na mutunta huldar abokantaka tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, Sin da Najeriya aminan juna ne, abokan arziki, kuma 'yan uwa na kwarai har abada. (Ahmed, Ibrahim /Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China