Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bikin rarraba kayayyakin tallafi da Sin ta baiwa kasashen Afrika a Habasha
2020-04-24 11:25:12        cri

Jiya Alhamis agogon Habasha, aka yi bikin rarraba kayayyakin tallafi da kasar Sin ta ba kasashen Afrika 12 a filin saukar jiragen sama na Bole dake Addis Ababa, fadar mulkin kasar.

Wadannan kayayyakin tallafi da gwamnatin kasar Sin ta ba kasashen Afrika sun isa Addis Ababa ne a 'yan kwanakin baya, kuma za a yi jigilarsu zuwa kasashen Angola da Kamaru da Afrika ta Tsakiya da kuma Chadi, har da Djibouti da kuma Lesotho da Madagascar sannan da Namibiya da Niger, da Rwanda da Somaliya da kuma Tanzaniya. Wadannan kayayyaki sun kunshi riguna da gilas na kandagarki da na'urorin gwada zafin jiki da abubuwan rufe baki da hanci da dai sauransu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China