Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen BRICS sun amince da inganta dangantakarsu dangane da yaki da COVID-19
2020-04-29 10:05:02        cri

Kasashen kungiyar BRICS masu saurin ci gaban tattalin arziki, sun amince su kara inganta dangantakarsu wajen yaki da annobar COVID-19.

An cimma matsayar ce jiya da yamma, yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen da aka yi ta kafar bidiyo.

Wang Yi, wanda kuma mamba ne na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya yi kira ga kungiyar BRICS ta dauki matakin da ya dace a lokacin da ya dace, bisa la'akari da yadda cutar COVID-19 ke mummunar barazana ga rayuka da lafiyar mutane a fadin duniya.

Ya kuma karfafawa kasashen gwiwar bunkasa hadin kai kan muhimman manufofin raya tattalin arziki da raya dangantakarsu domin kiyayewa da tabbatar da kamfanoni a duniya na aiki tare da samar da kayayyaki yadda ya kamata.

Wang Yi ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take, ta inganta gabatar da bayanai da fasahohinta ga kasashen BRICS tare da hada hannu wajen gudanar da bincike da samar da magunguna da alluran rigakafi, bisa mutunta cikakken 'yancin da yanayin kasashen juna.

Yayin taron, ministocin sun kuma yi tattaunawa mai zurfi, kan musayar ra'ayi dangane da kare tsarin huldar kasa da kasa da yaki da COVID-19 da kara bunkasa dangantakarsu. Har ila yau, sun amince da matse kaimi wajen musayar bayanai da fasahohi, da karfafa hadin gwiwa domin bada gudunmuwa wajen tsaron lafiyar al'ummar duniya da takaita mummunan tasirin annobar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China