Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta samu adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da COVID-19 a rana guda
2020-04-29 12:28:15        cri

A daren Talata Najeriya ta sanar da rahoton mutane 195 da suka kamu da annobar COVID-19 cikin sa'o'i 24, wanda shi ne adadi mafi yawa da aka samu a rana guda na mutanen da suka kamu da annobar a kasar mafi yawan jama'a ta yammacin Afrika, tun bayan samun rahoton farko na wanda ya kamu da cutar a karshen watan Fabrairu.

Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasar (NCDC) ta tabbatar da cewa, ya zuwa karfe 11:50 agogon kasar, na daren Talata, Najeriya tana da yawan mutanen da suka kamu da annobar 1,532.

Haka zalika, mutane 44 sun mutu yayin da mutane 225 suka warke ya zuwa yanzu.

Cikin sabbin rahoton da aka samu na wadanda suka kamu da cutar, har da babban birnin kasar da kuma wasu jahohi 14. Kawo yanzu cutar ta bulla a jahohin kasar 33 gami da babban birnin tarayyar Najeriya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China