Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala taron musamman na ministocin harkokin wajen BRICS.
2020-04-29 20:08:29        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana yau Laraba cewa, ministocin harkokin wajen kasashen BRICS sun kammala taro na musamman da suka kira tare da aike sako mai karfi cewa, kasashen biyar za su kara sadaukar da kai da yin hadin gwiwa ta yadda za su yaki annobar COVID-19 tare, hakan na da muhimmiyar ma'ana.

Geng ya bayyana haka ne a taron manema labarai a birnin Beijing, lokacin da yake mayar da martani kan rahotanni da kafafen watsa labarai suka watsa a baya-bayan game da kafa dakunan binciken sinadarai masu guba da Amurka ta yi a wasu yankunan tsohuwar tarayyar Soviet. Ya ce, yana fatan Amurka za ta nuna halin ya kamata, ta kalli abubuwan da ke damun duniya da rayuka, da lafiya da ma tsaron jama'a, ta dauki matakan da suka dace don kawar da shakkun da al'ummomin kasa da kasa ke da shi.

Dangane da rahoton da hukumar kula da 'yancin addinai ta kasa da kasa ta Amurka wadda ta zargi 'yancin addinai na kasar Sin kuwa, Geng Shuang ya ce, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta shaidu, ta yi watsi da girman kai da neman bata sunan kasar Sin, kana ta daina kafewa da batun addini tana tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China