Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar al'adun kasar Sin dake Mauritius ta samar da hidima ta yanar gizo ga jama'ar wurin
2020-04-30 13:25:16        cri

Tun bayan da aka gano mutum na farko da ya kamu da cutar COVID-19 a kasar Mauritius a ranar 18 ga watan Maris, gwamnatin kasar ta dauki tsattsauran matakai ba tare da bata lokaci ba, ciki har da killacewa a gida, dakatar da karatu a makarantu, rufe wuraren nishadi, da hana fita da dare da dai sauransu. Cibiyar al'adun kasar Sin dake Mauritius kuma ta gudanar da tsarin gaggawa na tinkarar annobar cikin sauri, da dakatar da dukkan ayyukan ba da horo, kana da fara gudanar da ayyukan mu'amala masu yawa ta yanar gizo, ta hakan aka samar da sabuwar hidimar gwaji ga jama'ar Mauritius da aka killace a gida.

A yayin da jama'ar kasar Mauritius ke kokarin yakar cutar COVID-19, cibiyar al'adun kasar Sin dake kasar ta mayar da martani cikin sauri, inda ta fara gudanar da tsarin gaggawa na tinkarar annobar, da kirkiro da sabuwar hanyar ayyuka, ciki har da amfani da dandalin sabbin kafofin watsa labaru na yanar gizo, don gudanar da ayyukan cudanyar al'adu da na ba da horo.

 

A cikin wadannan ayyukan, aikin "Tafiya a kasar Sin ta yanar gizo" ya yada labarun yawon shakatawa a kasar Sin ta hanyoyin yin nune-nunen hotuna da bidiyo game da yawon shakatawa a Sin, hakan ba ya bukatar su fita waje, jama'ar Mauritius sun iya yawon shakatawa a kasar Sin, ta hanyar kallon shahararrun wuraren kasar, da kuma fahimtar al'adun gargajiyar kasar ta yanar gizo. Sakataren cibiyar Hu Zihao ya ce, wannan aiki ya samu karbuwa da yabo sosai daga wajen jama'ar Mauritius. Ya kara da cewa,

"Mun yi amfani da wannan lokaci, wato na zaman gida, don nuna bidiyon fadakarwa guda biyar game da yawon shakatawa a kasar Sin, mun kuma shirya nune-nunen hotuna game da yankin Kuqa na jihar Xinjiang. Bisa kididdigar da muka yi, aikin nan da muka gudanar ya shafi mutane kusan dubu 10, inda suka tattauna sosai da kuma isar da aikin a yanar gizo, bayan wani mai kallo ta yanar gizo a kasar Mauritius ya kalli bidiyo game da tafiya a lardin Hainan na kasar sin, ya rubuta cewa, zai shigar da lardin Hainan cikin jerin sunayen wuraren da zai yi yawon shakatawa."

 

Yanzu ana samun yaduwar COVID-19 a duniya baki daya, amma an samu sassaucin yanayin dakile cutar sannu a hankali a kasar Sin, hakan ya sa fasahohin da Sin ta samu na yakar cutar, da labarum yakar cutar na jama'ar kasar suke jan hankulan jama'ar Mauritius. Don haka, cibiyar al'adun kasar Sin dake Mauritius ta kaddamar da jerin shirye-shiryen bincike game da yadda kasar Sin ke tinkarar annobar. Hu Zihao ya gabatar da cewa, labarun yakar cutar da aka bayyana a cikin bidiyon, sun taimaka wa jama'ar Mauritius kara fahimtar matakan da kasar Sin ta dauka na tinkarar annobar, kana sun kara musu kwarin gwiwar cimma nasarar yakar cutar.

"A cikin shirye-shiryen, an tattauna tare da wasu mutanen da suka shiga ko kuma suka sa ido kan yadda kasar Sin ke yakar cutar COVID-19. Ta hanyar bayyana labarunsu kai tsaye, jama'ar Mauritius sun kara fahimtar labaru masu burgewa na yakar cutar bisa hadin kai tsakanin gwamnatin kasar Sin da jama'arta."

 

Ban da wannan kuma, a lokacin dakile annobar, domin ci gaba da aikinta na koyarwa, malaman cibiyar al'adun kasar Sin suna amfani da dandalin yanar gizo don ba da darrusa ga dalibansu masu koyon Sinanci, hanyar kuma ta samu karbuwa daga daliban. Malamin cibiyar Ma Liang ya bayyana cewa,

"Yanzu dai, malamai biyu na cibiyarmu suna koyar da azuzuwa guda 6, ana ba da darrusa na sa'o'i 2 zuwa 3 ga ko wane aji a ko wane mako. Daliban dake karatu a nan sun fito daga fannoni daban daban na kasar ta Mauritius, ciki har da 'yan kasuwa, likitoci, masu harhada magunguna, masu tsara gine-gine da dai sauransu, har ma da 'yan asalin kasar Sin dake kasar da suka riga suka yi ritaya. Daliban sun ce, irin hanyar ba da darasi ta yanar gizo, ba taimaka musu wajen hana fita waje da tabbatar da tsaronsu kadai ya yi ba, har ma da taimakonsu wajen ci gaba da karatu, kana da kyautata yanayin zaman rayuwarsu na killacewa a gida, da sassauta tashin hankalin da suke fuskanta sakamakon yaduwar annobar. A hakika dai, koyarwa ta yanar gizo, ba kawai hada kan malamai da dalibai a wannan yanayin dakile cutar ya yi ba, abun ya fi muhimmanci shi ne, ya karfafa gwiwar kasashen Sin da Mauritius wajen yakar annobar." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China