Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rokoki uku da za a yi amfani da su wajen aikin gina tashar sararin samaniya ta kasar Sin
2020-05-06 11:51:13        cri

Bayan gwajin tashin da ya yi nasara, yanzu haka rokar Long March-5B da kasar Sin ta kera, ta hade da rokar Long March-2F da Long March-7 don gudanar da aikin gina tashar sararin samaniya ta kasar Sin.

Ita dai rokar Long Mach-2F, ita ce roka mafi tsaro da kasar Sin ta kera, tsayin ta ya kai kimanin mita 58, kana tana da manyan matakai guda biyu da injuna masu kara mata karfi guda 4. Za kuma a kafa wata hasumiyar kota kwana a samanta, yayin da aka yi amfani a rokar wajen harba kumbon dake dauke da 'yan sama jannati.

Babban injiniyan da ya tsara rokar Zhang Zhi, na cibiyar harba kumbunan kimiyya dake karkashin hukumar nazarin kimiyya da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin, ya ce, rokar za ta iya tashi da kayan da ya kai nauyin tan 480, za kuma ta iya aika kayan da nauyinsu ya kai tan 8.6 zuwa sararin samaniya. An tsara rokar ce, ta yadda za ta kasance mafi tsaro da tabbaci wajen dakon kaya.

A ranar 20 ga watan Nuwanban shekarar 1999 ce, aka yi amfani da rokar a karon farko, wajen harba kumbon Shenzhou-1 ba tare da matuki ba. A ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2003 ne aka yi amfani da rokar wajen harba dan sama jannatin kasar Sin na farko Yang Liwei zuwa sararin samaniya, abin da ya sanya kasar Sin zama kasa ta uku dake iya aika 'yan sama jannti zuwa sararin samaniya.

Babban darektan tawagar tsara rokar binciken sararin samaniya na kasar Sin, Jing Muchun ya ce, a cikin shekaru sama da 20 da suka gabata, rokar Long March-2F, ta kammala zirga-zirga 13 cikin nasara 100 bisa 100, inda aka yi amfani da ita, wajen harba kumbunan bincike 11 da dakunan gwaje-gwajen kimiyya 2 zuwa sararin samaniya.

Rokar Long March-7, roka ce ta musamman a fannin dakon kaya, tsayinta ya kai mita 53, tana da muhimman matakai guda biyu da suka kai fadin mita 3.35 da injuna guda hudu da fadinsu ya kai mita 2.25.

Man da rokar ke amfani da shi ba ya gurbata muhalli, ciki da iskar Oxygen mai ruwa-ruwa da Kalanzir. Nauyin tashinta ya kai kimanin tan 597, za kuma ta iya daukar kayan da ya kai kimanin tan 13.5 zuwa kasan falaki da kuma kayan da ya kai nauyin tan 5.5 zuwa kusa da kewayan rana dake cikin sararin samaniya.

An tsara rokar ta yadda za ta iya harba kumbon dakon kaya da kasar Sin ta kera. Bayan kammala gwajin tashi na farko cikin nasara a shekarar 2016, an yi amfani da rokar wajen harba kumbon dakon kaya na kasar Sin na farko mai suna Tianzhou-1, inda ya hade da dakin binciken sararin samaniya na Tiagong-2 a shekarar 2017.

Babban darektan tawagar bincken rokar Long March-7 Meng Gang, ya bayyana cewa, za a yi amfani da rokar ce, wajen dakon kayayyakin aikin gina tashar sararin samaniya ta kasar Sin, ciki har da kayayyakin da 'yan sama jannati za su amfani da su, kamar ruwan sha da abinci da rigunan 'yan sama jannati, da kayayyakin aiki da na gyara, kamar faranten hasken rana da kayan gyaransu

Meng ya kara da cewa, za a yi amfani da rokar wajen harba kumbon binciken sararin samaniya, wajen zuba mai a tashar binciken sararin samaniyan.

Kasancewarta roka ta farko da kasar Sin ta tsara bisa fasahar kimiyyar kere-kere, kana ta farko da aka harba a cibiyar harba kumbunan sararin samaniya ta Wenchang dake gabar kudancin tsibirin lardin Hainan, Rokar Long March-7, ta yi nasara daban-daban a jerin fasahar kirkire-kirkire, a cewar babban mai tsara rokar Fan Ruixiang.

Rokar Long March-5B, ita ce kashin bayan aikin gina tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin, Tsayin ta ya kai kimanin mita 53.66, kana fadinta ya kai mita biyar kana tana da injuna guda hudu da suka kai girman mita 3.35. Nauyin tashin ta zai kai tan 849, da kayan da ya kai nauyin kimanin tan 1,078, za kuma ta iya sauke kayan da ya kai nauyin a kalla tan 22 a sararin samaniya

Yanzu haka, ita ce roka mafi girma cikin rokokin da kasar Sin ta kera, inda tsayinta ya kai mita 20.5 da fadin mita 5.2, kana tsayinta ya kai gini mai hawa 6.

Babban darektan tawagar aikin binciken tsara rokar Wang Jue, ya ce, an tsara rokar ce, musamman don harba kumbuna da kumbunan gwajin tashar binciken sararain samaniya ta kasar Sin. Kana za ta kasance kashin bayan aikin gina tashar.

Babban mai aikin tsara rokar Li Dong, ya ce, tawagar binciken tsara rokar, ta cimma nasarori a fannonin fasahar kere-kere, kamar raba rokoki daga aikin sauke kaya a sararin samaniya da magance kuskuren lokacin harba roka cikin dakika 1.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China