Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta isar da masanan kimiyya kolin babban dutsen Himalayas bisa fasahohin zamanin yanzu
2020-05-11 11:41:47        cri

A ranar 10 ga wata, a lokacin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon CRI, Mr. Wang Yongfeng wanda ke kula da aikin hawa babban dutsen Himaliyas, da kuma aikin safiyon tsayin dutsen a bana, ya bayyana cewa, yanzu masu wasan hawa manyan duwatsu na kasar Sin suna iya cewa, za su iya isar da masanan kimiyya kolin babban dutsen Himaliyas, wato Jomolama, bisa fasahohin zamani, kamar fasahar sadarwa ta 5G. Sakamakon dusar kankara da ake da ita a kan hanyar hawa babban dutsen Himalayas, a ranar 9 ga watan Mayu, tawagar hawa da kuma safiyon tsayin kolin babban dutsen Himalayas ta kasar Sin ta sanar da cewa, za a jinkirta lokacin hawa dutsen.

Mr. Wang Yongfeng wanda yake kulawa da wannan aiki na hawa da kuma safiyon babban dutsen, yana mai cewa, "An samu dusar kankara mai tsanani sosai a bana. Ba mu iya isar da ma'aikatan gyara hanya da kuma na safarar kayayyaki kolin babban dutsen ba. Sakamakon haka, ba za mu iya kaddamar da aikinmu a ranar 12 ga wata ba, wato rana mafi dacewa ga aikin. Yanzu dukkan ma'aikatan kula da aikin safiyon babban dutsen sun koma sansaninmu dake kan babban dutsen. Muna jiran yanayi mafi dacewa."

Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta sake safiyon tsayin kolin babban dutsen Himalayas bayan shekaru 15 da suka gabata. Kawo yanzu an kirkiro da kuma samo dimbin fasahohin zamani. Alal misali, masanan kimiyya za su yi amfani da na'urorin safiyo kirar kasar Sin wajen safiyon babban dutsen bisa tsarin sadarwa na taurarin dan Adam na Beidou da kasar Sin ta kafa a sararin samaniya da sauran fasahohin zamani da kasar Sin take da su yanzu, ta yadda za ta iya samun karin bayanan babban dutsen kamar yadda ake fata.

Mr. Wang Yongfeng, wanda ya taba hawan kolin Jomolama na babban dutsen Himalayas har sau 3, ya ce, suna fuskantar sabbin kalubaloli biyu da dole sai an shawo kansu.

"Da farko dai, muna bukatar isar da wasu na'urorin safiyo na zamani kolin babban dutsen, har ma mu yi amfani da su a kolin. Bugu da kari, dole ne mu isar da masanan kimiyya kolin lami lafiya, har ma mu tabbatar da ganin sun gwada da kuma yin amfani da wadannan na'urori wajen aikin safiyo a kolin lami lafiya. Su ne kalubale mai tsanani da jarrabawa dake gaban tawagarmu ta hawan manyan duwatsun."

Wang Yongfeng ya bayyana cewa, yanzu kayayyakin hawa babban dutsen Himalayas sun samu kyautatuwa sosai idan an kwatanta su da na da. Tun daga shekarar 2003, makarantar koyon fasahohin hawan manyan duwatsu ta Tibet, wadda aka kafa a shekarar 1999, ta samu dukkan ayyukan ba da tabbas ga aikin hawan babban dutsen Himalayas daga arewacin dutsen. Cikkaku da ingantattun kayayyakin da tawagar hawa manyan duwatsu ta kasar Sin take samu yanzu, su ne kuma ke karfafa gwiwar masu hawa dutsen wajen isar da masanan kimiyya kolin Jomolama na babban dutsen Himalayas.

Mr. Wang Yongfeng ya bayyana cewa, "Sakamakon irin wadannan kayayyaki da na'urorin zamanin da ake da su, muna iya ba da tabbacin cewa, za mu iya isar da masanan kimiyya kolin babban dutsen Himalayas lami lafiya. A hakika dai, akwai hadari wajen isar da masanan kimiyya kolin babban dutsen Himalayas, amma sabo da a yanzu makarantar koyon fasahohin hawan manyan duwatsu ta Tibet tana da fasahohin zamani na ba da tabbaci ga aikin hawan babban dutsen, muna iya gabatar da wannan burin da za mu iya cimmawa, ta yadda za mu iya samun wani babban ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi."

Mr. Wang Yongfeng ya ba da misali cewa, a da, a lokacin da muka hau kan kolin Jomolama na babban dutsen Himalayas, masu hawa dutsen sun yi amfani da wayar salula ta tafi da gidanka, wato Walkie-talkie, amma yanzu, za su yi amfani da wayar salula ta 5G a lokacin da suke mu'amala da wadanda suke aiki a sansanin tawagarsu. Za a iya tabbatar da ganin an samu nasarar hawan babban dutsen Himalayas lami lafiya bisa wannan fasahar sadarwar ta 5G. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China