Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya jaddada tabbatar da gina zamantakewar al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannonii
2020-05-13 14:19:04        cri






Daga ranar 11 zuwa 12 ga wata, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kana shugaban kasar Xi Jinping, yayi rangadi a biranen Datong da Taiyuan na lardin Shanxi na kasar, inda ya ziyarci gandun noma, da sabon kauyen da aka gina don tsugunar da masu fama da talauci, da kuma kamfani, don fahimtar yadda ake gudanar da ayyukan kandagarkin cutar Covid-19, da bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma, da kuma kiyaye nasarorin da aka cimma wajen saukaka fatara.

A ranar 11 ga wata da yamma, shugaba Xi Jinping ya fara ziyararsa ne daga yankin Yunzhou da ke birnin Datong, inda ya ziyarci wata gonar noman tsiron Daylily. Birnin Datong yana da tarihi na sama da shekaru 600 na noman tsiron Daylily, wanda ya zama wani ginshiki na tattalin arzikin wurin, wanda a bara ya samar wa kowane magidanta da ke fama da talauci na yankin kudin shigar da ya kai sama da yuan dubu 10.

Yayin ziyarar, shugaba Xi ya kewaya gonar, tare da tattaunawa da ma'aikatan dake aiki a ciki, ya kuma yi farin cikin ganin cewa, a shekarun baya-bayan nan, ana samun amfanin gona mai armashi da inganci, wanda ke da tsayayyar kasuwa da farashi. Xi ya ce, noman tsiron Daylily ka iya zama babbar sana'a mai dimbin riba. Yana mai cewa, "Noman tsiron Daylily ka iya zama babbar sana'a mai dimbin riba, da makoma mai kyau. Ku yi kokarin karewa, da raya sana'ar noman Daylily tare da ba ta damar taka rawa wajen yaki da talauci."

Sabon kauyen Fangcheng da ke yankin Yunzhou, kauye ne da aka gina musamman domin tsugunar da masu fama da talauci. Akwai magidanta 77 masu fama da talauci da aka fara tsugunar da su a kauyen tun daga shekarar 2018, wadanda kuma dukkaninsu suka fita daga dangin talauci bisa sana'ar noman daylily.

Malam Bai Gaoshan na daya daga cikin mazauna kauyen, kuma a gidansa ne shugaba Xi Jinping ya zauna tare da shi da iyalansa suka kuma zanta. Malamin ya ce, a baya shi da iyalansa na zama ne cikin gidajen kogo, amma ga shi an gina musu sabon gida, wanda ke kusa da inda suke aiki, rayuwarsu ma ta inganta matuka. A bara, dansa ya yi aure, a wannan shekara kuma Allah ya albarkace su da jika. Shugaba Xi Jinping ya yi farin ciki da cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin jam'iyya ce da ke bautawa al'umma, kuma a maimakon ta bukaci masu fama da talauci su biya haraji, tana samar musu magunguna, da fasahohi, da kuma dabaru na fita daga kangin talauci. Ya ce, rayuwar mazauna kauyen za ta kara kyautata a nan gaba. Ya kara da cewa, bana shekara ce da ake sa ran cimma burin saukaka fatara, da ma gina al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni, kuma za a yi iyakacin kokarin kiyaye nasarorin da aka cimma wajen saukaka fatara, tare da kara mai da hankali a kan raya karkara, ta yadda al'umma za su kara jin dadin rayuwarsu.

Da ya bar kauyen, mazauna kauyen sun yi ban kwana da su, shugaba Xi Jinping ya kuma yi musu fatan alheri na jin dadin rayuwarsu.

A safiyar yau Talata 12 ga wata, shugaba Xi Jinping ya ziyarci kamfanin samar da karafa na birnin Taiyuan wato TISCO, kamfanin da ya samu saurin ci gaba sakamakon fasahohinsa na samar da karafa. Yayin ziyarar, Xi ya bayyana cewa, "Na yi farin ciki matuka da ganin yadda fasahohin zamani suka ci gaba cikin sauri a lardin Shanxi, kamfanin TISCO shi ma ya ci gaba matuka a bangaren kirkire-kirkiren fasaha, kana matsayinsa ya inganta yadda ya kamata, ina fatan za ku kara samun sabbin ci gaba a fannin samar da karafa."

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, yanzu an kai wani sabon mataki wajen yaki da cutar Covid-19 a fadin duniya, inda baya ga gagaruman nasarorin da aka cimma, ana kuma fuskantar kalubale na shigowar cutar daga ketare da kuma farfadowar cutar a cikin gida, don haka ya yi fatan kamfanin zai dauki managartan matakai na kandagarkin cutar, ta yadda za a kare lafiyar ma'aikata, don su dawo bakin aiki ba tare da wata matsala ba.(Lubabatu)
 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China