Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin WHO dake kasar Sin ya rubutawa daliban Wuhan wasika
2020-05-14 10:55:22        cri
Kwanan baya, wasu daliban makarantar Xuguang dake birnin Wuhan na kasar Sin, sun rubuta wata wasika zuwa ga wakilin hukumar lafiya ta duniya WHO dake kasar Sin, Dokta Gauden Galea, wasikar da ta burge shi, gami da abokan aikinsa kwarai da gaske. Har ma Mr. Gauden Galea ya rubuta wasika cikin yaren Sin zuwa ga wadannan daliban.

A cikin wasikar tasa, Dokta Gauden Galea ya ce, ya samu wasikar a daidai lokacin da ya cika shekaru biyu da zama wakilin WHO a kasar Sin. A cewarsa, wasikar ta tunatar da shi game da mutane da dama da ya hadu da su a kasar, musamman ma'aikatan lafiya wadanda suka yi namijin kokarinsu wajen inganta lafiya da tsaron al'ummar kasar, da na duniya baki daya.

Ya ce, abun alfahari ne gare shi, gudanar da ayyuka tare da su, musamman tun barkewar cutar mashako ta COVID-19. Bugu da kari, jama'a daga sassa daban-daban na kasar Sin sun yi masa kirki sosai.

Wasikar ta kara da cewa, annobar COVID-19 kalubale ne ga kowa da kowa, amma ta shaidawa duk duniya kyawawan halayen al'ummar kasar Sin daga bangarori da dama, ciki har da dagewa, nuna kauna, da kuma son taimakawa saura. Ya ce, akwai al'ummar kasar Sin da yawa, ciki har da daliban makarantar Xuguang dake Wuhan, wadanda a shirye suke su samar da taimako ga sauran kasashen duniya.

A karshen wasikar, Dokta Gauden Galea ya yi fatan daliban makarantar Xuguang dake birnin Wuhan za su ji sahihancinsa, kamar irin sahihancin da ya ji lokacin da ya samu wasika daga gare su.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China