Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ayyukan sa idon da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yi sun taimaka ga ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma
2020-05-18 14:41:37        cri


Aikin sa ido, wani muhimmin iko ne da kundin tsarin mulki gami da dokokin kasar Sin ya baiwa zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar. Tun lokacin da aka kira zama na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, majalisar take kokarin aiwatar da aikin sa ido domin tabbatar da ci gaban tattalin arziki gami da zaman rayuwar al'umma.

Delongweiyong, wata muhimmiyar magudanar ruwa ce dake kudancin garin Humen na birnin Dongguan a lardin Guangdong, wadda daya ne daga cikin kogunan da aka mai da hankali a kan tsaftace ruwansu. Yanzu ingancin magudanar ruwan ya kyautata sosai duba da irin kwararan matakan da rukunin bincike na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya dauka, inda aka tuhumi wasu kamfanoni 25 da laifin gurbata muhalli.

Kamfanin samar da kayan karafa na Jieye dake birnin Dongguan, ya kammala aikin gyara laifinsa kamar yadda aka bukace shi da ya gudanar da ayyuka ba tare da gurbata muhalli ba. Babban manajan kamfanin, Mista Yi Jinsong ya bayyana cewa:

"Tsauraran matakan da aka dauka, musamman matakin sa ido, abu ne mai kyau. Mun saka kudin kiyaye muhalli a cikin dukkan kudaden da muka kashe wajen gudanar da ayyukan kere-kere, al'amarin da zai taimaka sosai ga bunkasuwar sana'armu gami da kyautatuwar muhalli. Yanzu kamfaninmu na iya gudanar da ayyukanmu cikin kwanciyar hankali."

Domin gudanar da ayyukan kiyaye muhallin halittu yadda ya kamata, rukunin gudanar da bincike na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi tattaki zuwa wasu larduna 8 a bara, don nazarin muhimman wuraren dake fama da matsalar gurbatar muhalli.

Kwamishinan kiyaye muhallin halittu na lardin Jiangsu, Mista Wang Tianqi ya bayyana cewa:

"Sakamakon binciken da aka gudanar, lardin Jiangsu ya bullo da dokar sa ido kan muhallin halittu, dokar da ta zama ta farko a wannan fanni a matakin lardi a kasar."

Har wa yau, rukunin ya gudanar da bincike kan yadda ake aiwatar da wasu dokoki biyar da suka shafi raya kamfanoni matsakaita da kanana, da kara samar da guraban ayyukan yi, a wani mataki na tabbatar da cewa, ana aiwatar da manufofin jam'iyyar kwaminis gami da dokokin kasar yadda ya kamata.

Jami'in sashen binciken yadda ake aiwatar da doka na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Cheng Lifeng ya ce:

"Rukuninmu na sa ido sosai kan yadda ake aiwatar da wasu muhimman dokoki, da zummar gano matsalolin da ake fuskanta, da lalibo musabbinsu, domin tabbatar da aiwatar da su daidai bisa tsari."

Sa ido kan yadda aka kashe kudaden jama'a shi ma wani muhimmin aiki ne na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. A shekara ta 2018, a karon farko zaunannen kwamitin majalisar ya saurari rahoton da majalisar gudanarwa ta gabatar dangane da kadarorin kasa, sa'an nan a bara, a karon farko an gabatar da wani rahoto na musamman kan yadda hukumomin gwamnati suka kula da kadarorin kasa ga zaunannen kwamitin majalisar don ya duba.

Jami'in dake aiki a ofishin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Jincheng ya nuna cewa, ayyukan sa ido kan yadda ake kula da dukiyar kasa, sun shaida irin babban nauyin dake wuyan majalisar na tafiyar da ikon sa ido, inda ya ce:

"Bayan da aka bullo da tsarin gabatar da rahoto kan sarrafa dukiyar kasa da majalisar gudanarwa ta yi ga zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar, zaunannen kwamitin yana gudanar da ayyukan sa ido daidai bisa doka. Majalisar gudanarwa tana tafiyar da ikon kula da dukiyar kasa a madadin gwamnati, shi kuwa zaunannen kwamitin majalisar yana sa ido kan yadda ake amfani da dukiyar kasa a madadin daukacin al'ummar kasar."

Tun bayan da aka yi zama na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, zuwa yanzu, zaunannen kwamitin majalisar ya saurari rahotanni da dama, wadanda suka shafi batutuwan kiyaye muhalli, da samar da ilimin yara kafin shiga makaranta, da samar da agaji ga al'umma da sauransu.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China