Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Kenya: Sin na taka babbar rawa yayin dakile COVID-19 a duniya
2020-05-20 10:31:19        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda shida, kuma ya sanar da matakai guda biyar a bangaren yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 yayin babban taron kiwon lafiyar duniya karo na 73 da aka kira ta kafar bidiyo, haka kuma ya bayyana cewa, kasarsa za ta kara goyon bayanta da take nunawa kasashen Afirka yayin da suke kokarin dakile annobar, kan wannan, masani a jami'ar Nairobin kasar Kenya Gerrishon Ikiara ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu na CMG cewa, kasar Sin tana taka babbar rawa a yakin da ake da annobar a fadin duniya.

Masanin jami'ar Nairobin Kenya Gerrishon Ikiara ya bayyana cewa, tsarin kiwon lafiyar kasashen Afirka ba shi da inganci, a don haka suna bukatar goyon bayan kasar Sin, hakika al'ummun kasashen nahiyar suna godiya matuka ga tallafin kasar Sin, kana yana ganin cewa, dalilin da ya sa Amurka ta zargi kasar Sin shi ne tana son siyasantar da annobar.

A cikin jawabinsa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawara cewa, ya dace kasashen duniya su samar da karin tallafin kayayyaki da fasahohi da kwararru ga kasashen Afirka yayin da suke kokarin kandagarkin annobar COVID-19, kana ya bayyana cewa, kawo yanzu kasar Sin ta riga ta samar da kayayyakin kiwon lafiya masu dimbin yawa ga kungiyar tarayyar Afirka da ma kasashen Afirka da yawansu ya kai sama da 50, ban da haka, ta tura tawagogin kwararrun likitoci guda biyar zuwa kasashen nahiyar. A cikin shekaru 70 da suka gabata, gaba daya adadin al'ummun kasashen Afirka wadanda suka taba samun jinyar likitocin da gwamnatin kasar Sin ta tura ya kai sama da miliyan 200, kan wannan, Ikiara ya nuna cewa, tun bayan da kasashen Afirka suka fara fama da annobar Ebola, har kullum kasar Sin tana samar musu da tallafi gwargwadon karfinta, yanzu haka annobar COVID-19 ta barke a nahiyar, kasar Sin tana ci gaba da samar musu da tallafin kayayyakin kiwon lafiya, har ta tura tawagogin kwararrun likitoci zuwa kasashen, Ikiara ya kara da cewa, al'ummun kasashen Afirka suna godiya matuka ga tallafin kasar Sin, yana mai cewa, "Kasar Sin tana taka babbar rawa a yakin da ake da annobar COVID-19, tun bayan barkewar annobar, kasar Sin ta dauki makatan da suka dace nan take ba tare da bata lokaci ba, shi ma shugaban kasar Sin yana tuntubi takwarorinsa na kasashen Afirka domin tattauna yadda za a ga bayan annobar nan da nan. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin da kasashen Afirka suna gudanar da hadin gwiwa cikin lumana, yanzu haka gwamnatin kasar Sin da kungiyoyin kasar masu zaman kansu suna samar mana da tallafi gwargwadon karfinsu, muna godiya matuka."

Shugaba Xi shi ma ya sanar da cewa, kasar Sin za ta bullo da tsarin hadin gwiwa tsakanin asibitocin sassan biyu guda 30, tare kuma da kyautata aikin cibiyar CDC, ta yadda za a kara karfin kandagarkin cututtuka na kasashen. Kan batun, Ikiara ya bayyana cewa, goyon bayan da kasar Sin take baiwa kasashen Afirka yana da muhimmanci kwarai, saboda tsarin kiwon lafiya na kasashen ba shi da inganci, kana yana fatan cewa, nan gaba kasar Sin da kasashen Afirka za su kara hadin gwiwarsu a fannin samar da kayayyakin kiwon lafiya, a cewarsa: "Kasashen Afirka suna fatan za su yi hadin gwiwa mai dorewa da kasar Sin, musamman ma a bangaren musanyar kwararrun likitoci da samar da kayayyakin kiwon lafiya, muna fatan kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen Afirka domin raya sana'o'in samar da kayayyakin kiwon lafiya, saboda yana da wahala a kawo karshen annobar cikin gajeren lokaci."

Game da zargin da Amurka ta yi kan kasar Sin kan asalin kwayar cutar COVID-19, Ikiara yana ganin cewa, Amurka tana siyasantar da annobar ce, dalilin da ya sa haka shi ne Amurka ba ta dauki matakan da suka dace ba yayin bazuwar annobar, yana mai cewa, "An saurari wasu sanarwoyin da gwamnatin Amurka ta fitar kan annobar, hakika ba su da ma'ana ko kadan wajen daidaita matsalar, sun bayyana cewa, sun riga sun yi bincike, amma ba su gabatar da shaidun dake nuna cewa, kwayar cutar COVID-19 ta samo asali ne a kasar Sin , Amurka tana son siyasantar da annobar, har ma ta yi kashedi cewa, za ta fice daga hukumar lafiya ta duniya, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen kare lafiyar al'ummun kasa da kasa, hakika duk wadannan za su lahanta muradun al'ummun kasar ta Amurka ita kanta."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China