Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin
2020-05-22 15:33:54        cri





A yau Jumma'a, aka bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, majalisar da ta kasance hukumar koli ta kasar. Shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da sauran shugabannin kasar sun halarci taron. An jinkirta taron zuwan watan Mayu da muke ciki, sakamakon annobar Covid-19, karon farko da aka taba jinkirta taron cikin shekaru 22.

A wannan rana, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoto dangane da yadda gwamnati ta gudanar da aiki tun daga shekarar 2019 kawo yanzu, da kuma muhimman ayyukan da za a sanya gaba, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ba ta tsoron barazana da kalubale, kuma tana da niyyar shawo kan illolin da cutar Covid-19 ke haifarwa, tare da cimma burin fid da dukkanin al'ummar da ke fama da talauci a yankunan karkarar kasar daga kangin da suke ciki, da kuma gina al'umma mai matsakaicin wadata. A wannan shekara, cutar Covid-19 da ta bulla ba zato ta shafi kasashe da shiyyoyin duniya sama da 210 da kuma al'ummar duniya sama da biliyan 7, kana ta halaka mutane sama da dubu 300. Bisa namijin kokarin da ta yi tare da munanan hasarorin da ta fuskanta, kasar Sin ta samu gaggaruman nasarori wajen shawo kan cutar.

A yayin zaman bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka gudanar a yau, an rera taken kasar Sin kamar yadda aka saba, kafin daga bisani, dukkan mahalarta taron sun yi tsit na tsawon minti guda, don girmama wadanda suka sadaukar da rayukansu a yaki da cutar Covid-19 da kuma 'yan kasar da cutar ta halaka.

A yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya, kasar Sin na fuskantar barazana da kalubale da ba a taba ganin irinsa ba ta fannin ci gabanta. A game da manufar da ake fatan aiwatarwa a nan gaba, rahoton aikin gwamnati da aka gabatar a taron ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan kandagarkin cutar, a yayin da take kokarin kiyaye manufar ci gabanta. Firaminista Li Keqiang ya ce,"A nan gaba, kasarmu za ta fuskanci kalubalen da ba mu taba gani ba, amma muna da tsarin tafiyar da harkokin kasa mai inganci, da kuma tushen tattalin arziki mai inganci, da babbar kasuwa, da kuma jama'a masu hazaka da hikima. Duk da kalubalen da muke fuskanta, muddin muka karfafa niyyarmu, da kara zage damtse kan raya kasa, da kuma yin amfani da damammakin da muke da su, hakika za mu haye wahalar da ke gabanmu, tabbas kuma akwai kyakkyawar makoma ga ci gaban kasar Sin."

Sai dai rahoton bai bayyana takamaiman adadin da ake fatan cimma wa dangane da ci gaban tattalin arziki a wannan shekara ba. A game da wannan, firaminista Li Keqiang ya ce, sabo da rashin tabbas din da ake fuskanta a fannonin yanayin yaduwar cutar a duniya da kuma tattalin arziki, shi ya sa kasar Sin take fuskantar rashin tabbas a fannin ci gabanta. Ya ce, "Hakan zai taimaka inda aka hada karfin bangarori daban daban wajen gudanar da aikin kiyaye wasu fannoni 6 da kuma tabbatar da wasu sassa 6. Tabbatar da fannoni shida zai taimaka ga tabbatar da tushen tattalin arziki, haka kuma zai taimaka ga kiyaye kwanciyar hankali da kuma ci gaba. Abin lura shi ne, tabbatar da samar da guraben aikin yi da zaman rayuwar al'umma da saukaka fatara da kuma daidaita hadarin da ake fuskanta, duk sun dogara ne ga ci gaban tattalin arziki, don haka, kiyaye ci gaban tattalin arziki na da matukar muhimmanci. Ya kamata mu martaba manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, mu kiyaye samar da guraben aikin yi da tabbatar da rayuwar al'umma, sa'an nan a sa kaimi a harkokin sayayya da kasuwanni tare kuma da kiyaye ci gaban tattalin arziki, don tinkarar matsalar da muke fuskanta."

Bana ita ce shekara ta karshe da ake fatan kammala aikin gina al'umma mai matsakaicin karfi da kuma aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13. Rahoton aikin gwamnati ya kuma jaddada cewa, ya kamata a tashi tsaye wajen cimma burin fitar da masu fama da talauci daga kangin da suke ciki, kuma ya kamata a dukufa a kan bunkasa ayyukan gona, da kyautata rayuwar manoma.

Rahoton ya kuma yi bayani game da manufofin kasar da suka shafi kabilu da addini, da tsaron kasa da raya rundunonin soja, da bunkasuwar yankunan musamman na Hong Kong da Macau da huldar da ke tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan, da kuma manufofin diflomasiyya na kasar. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China