Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana: Taruka 2 na kasar Sin za su sa kaimi ga kokarin farfadowar imanin duk duniya
2020-05-25 11:58:05        cri

A 'yan kwanakin baya, gamayyar kasa da kasa ta yi ta maida hankali kan taruka biyu, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar.

A lokacin da tattalin arzikin duniya yake fuskantar tasirin annobar cutar numfashi ta COVID-19, wadannan taruka biyu na kasar Sin sun jawo hankulan masana tattalin arzikin kasar Burtaniya. Mr. John Davie, tsohon shugaban kwamitin kula da dangantakar hadin gwiwa ta abokantaka tsakanin masana'antun mallakar gwamnati da na masu zaman kansu na gwamnatin kasar Burtaniya ya bayyana cewa, wadannan taruka biyu na kasar Sin za su taka rawar gani wajen karfafa gwiwar duk duniya. Gwamnatin kasar Sin ta yi la'akari sosai da tasirin da annobar COVID-19 ta haddasa, saboda haka, gwamnatin kasar Sin ta tsara burikan da za ta cimma a bana bisa hakikanin halin da ake ciki.

Mr. John Davie yana ganin cewa, "A ganina, burin da aka tsara a cikin rahoton gwamnatin kasar Sin zai sa kasar ta samu wani babban ci gaba wajen kashe karin kudade a cikin gidan kasar, a fannonin yaki da talauci, wato a lokacin da ake kashe karin kudade a gida, za a iya bayar da gudunmawa wajen yaki da talauci. Abu mafi muhimmanci ga jama'a shi ne, samar musu aikin yi, tare da kyautata zaman rayuwarsu kai tsaye."

Kwararriya Nadia Helmy, ta jami'ar Beni-Suef ta kasar Masar wacce ta kware kan nazarin harkokin kasar Sin ta gayawa wakilin CMG dake Alkahira cewar, ta fi maida hankali kan wasu matakan tattalin arziki da gwamnatin kasar Sin ta tsara a cikin rahoton gwamnatin.

Nadia Helmy ta ce, "A cikin rahoton da gwamnatin kasar Sin ta fitar, matakan shawo kan illar da annobar cutar numfushi ta COVID-19 ta haddasa domin kokarin farfado da tattalin arziki da tafiyar da ayyukan masana'antu a kai a kai, da kara tallafawa masana'antun kere-kere. Sannan da samar da rancen kudi ga kananan kamfanoni, ta yadda kudi zai iya taka rawa, da kuma samar da guraben aikin yi. Bugu da kari, matakan yaki da kangin talauci da na farfadowar yankunan karkara, sun burge ni sosai. Wadannan matakai sun bayyana yadda gwamnatin kasar Sin ta bada muhimmanci ga mutane masu karamin karfi da annobar ta kawo musu illoli."

Xulio Rios, direktan ofishin sa ido kan manufofin kasar Sin na kasar Sifaniya wanda ya kware kan batutuwan kasar Sin ya bayyanawa wakilinmu cewa, wadannan taruka biyu da aka jinkirtar lokacin gudanar da su a lokacin da ake yakar annobar COVID-19 sun fi jawo hankalin kasashen duniya. A lokacin da yake ambato burikan cimma nasarar fama da kangin talauci gaba daya a karshen shekarar 2020, ta yadda za a iya kafa wata al'umma mai matsakaiciyar wadata a kasar Sin, Xulio Rios ya ce, wadannan burika biyu suna da muhimmanci matuka. Yana cike da imanin cewa, ko da yake yanzu ana cikin hali mai tsanani, amma kasar Sin zata iya cimma wadannan burika biyu.

A yayin taron manema labaru da aka shirya a Lahadi, Mr. Wang Yi, dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar ya bayyana cewa, kasashen Afirka da kasar Sin sun kasance tamkar 'yan uwa ne dake da tarihi da makoma iri daya. Su kan yi hadin gwiwa a kan hanyar neman ci gaba. Mr. Kwesi Quartey, mataimakin shugaban kwamitin kungiyar AU ya nuna godiya ga goyon bayan da gwamnati da jama'ar kasar suka dade suna baiwa kasashen Afirka. Kasashen Afirka suna martaba zumuncin dake tsakaninsu da kasar Sin. Bayan barkewar annobar COVID-19, kasashen Afirka sun jinjinawa tallafin da kasar Sin ta samar musu.

Mr. Kwesi Quartey ya nuna cewa, "A kullum kasar Sin na goyon bayan Afirka. Kasar Sin ta goyi bayan gwagwarmayar neman 'yancin Afirka. Bunkasuwar da kasar Sin ta samu cikin lumana ta kasance tamkar wani misalin abin koyi ga kasashen Afirka, wato idan ana son samun bunkasuwa, ana bukatar daidaita tunanin falsafa da daidai shugabanci. Sabo da haka, muna martaba dangantakar da ta dade tana kasancewa tsakaninmu. Kasar Sin ta samarwa kasashen Afirka dimbin kayayyakin kandagarkin annobar, mun rabawa kasashenmu. Muna yiwa kasar Sin godiya. Bugu da kari, dole ne mu dauki matakai tare, ta yadda zamu iya kawar da zarge-zarge da jita-jita a fili kamar yadda ake fata." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China