Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin da Afirka suna goyon bayan ra'ayin ciniki marar kariya tsakanin kasa da kasa
2020-05-25 17:39:55        cri

Tun bayan kaddamar da muhimman taruka biyu na shekara-shekara na kasar Sin na bana, al'ummar kasa da kasa suka zuba ido domin lura da muhimman batutuwan da tarukan za su mayar da hankali musamman duba da yadda aka dage lokacin da aka saba gudanar da su saboda yanayin yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 wacce take ci gaba da yaduwa a duniya kamar wutar daji. A bisa al'adar tarukan biyu wakilan dukkannin yankunan kasar Sin da kwararru daga dukkan fannoni su kan tattaunawa al'amurran da suka shafi makomar kasar har ma da sauran batutuwa dake shafar tsarin diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasa da kasa. A mafi yawan lokuta kasar Sin tana yawan mayar da hankalinta kan batun da ya shafi makomar Afrika da kasashe masu tasowa. Manufar bude kofar Sin ga ketare yana daga cikin al'amurran da suka dauki hankali kasashen duniya musamman ra'ayin tsarin cudanya na bangarori daban daban a maimakon ra'ayin kashin kai da wasu kasashen yammacin duniya suke ikirari a mafi yawan lokuta. Wannan batu yana daga cikin batutuwan da mamban majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi, ya gabatar a matsayin wasu shawarwari guda 3 game da aikin kyautata tsarin kula da duniya, a wajen taron manema labaru da ya gudana a Lahadi, karshen wannan mako, a gefen tarukan majalisun kasar Sin da ke gudana a halin yanzu.

Bayan sauraron kalaman da mista Wang ya gabatar, wasu masana da manyan jami'ai na kasashen Afirka, sun nuna amincewa da manufar da kasar Sin ta gabatar, tare da nanata cewa, yunkurin adawa da dunkulewar duniya, da neman daukar matakan kariya na kashin kai, ba shi da alfanu ko kadan. Cikin wadannan manyan kusoshin, har da wani shehun malami mai nazarin batutuwa masu alaka da Afirka da Sin daga tarayyar Najeriya, mista Adekunle, wanda ya ce ya gamsu da kiran da kasar Sin ta yi na kafa al'umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil Adama ta fuskar kiwon lafiya, saboda wannan aikin ya shafi ingancin zaman rayuwar daukacin dan Adam. A cewarsa, yanzu haka dukkan mutanen duniya na kokarin yaki da annobar COVID-19, kana ba za a samu nasara a wannan yunkuri ba muddin ba'a yi watsi da bambancin kabila, da nuna kiyayya, kana a kuma karfafa hadin gwiwa tsakaninsu kasa da kasa ba, don neman ci gaban al'ummun duniya baki daya.

Shi kansa shugaba Xi Jinping na kasar Sin a lokacin da ya halarci cikakken zaman taron 'yan majalisar bada shawara kan harkokin siyasa mai kula da tattalin arzikin kasar Sin, ya jaddada cewa, a halin yanzu, wasu kasashen duniya sun nuna ra'ayin kariyar ciniki, amma kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan kare tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa da kuma raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa ra'ayin dimokuradiyya.

A nan gaba kuma, za ta ci gaba da neman bunkasuwa bisa ka'idojin bude kofa ga waje, da hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna, domin inganta bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta fuska mai bude kofa ga waje da fahimtar juna da cimma daidaito da kuma cimma moriyar juna, ta yadda za a gina tsarin tattalin arzikin duniya mai bude kofa ga waje. Hakika za'a iya cewa ra'ayi ya zamanto iri guda a tsakanin shugabannin Sin da na Afrika wajen nuna adawa da ra'ayin kashin kai a maimakon hada kai da juna domin cin moriyar juna don a gudu tare a tsira tare kasancewar hannu daya baya daukar jinka.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China