Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren jam'iyyar Jubilee ta Kenya: Ya dace a koyi fasahar Sin wajen yaki da talauci da COVID-19
2020-05-26 10:36:01        cri

Kwanan baya, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai cewa, kasashen Afirka 'yan uwan kasar Sin ne, wadanda ke da makoma ta bai daya.

A jiya Litinin, agogon kasar Kenya, babban sakataren jam'iyyar Jubilee mai mulki a kasar Raphael Tuju, ya yi zantawa da wakilinmu na CMG, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako wajen kubutar da al'ummar ta daga kangin talauci, da kuma yaki da annobar COVID-19, don haka ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin da kasar Sin ta samu.

Babban sakataren jam'iyyar Jubilee mai mulki a kasar Kenya Raphael Tuju ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban sakamakon da ya bai wa al'ummun kasa da kasa mamaki, wajen kubuta daga kangin talauci, da kuma yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, don haka ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin da kasar Sin ta samu a wadannan bangarori.

Yayin taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan duk jama'ar kasar, da kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, batu game da yadda za a cimma burin kubuta daga kangin talauci daga dukkanin fannoni kafin karshen shekarar bana a kasar, ya fi jawo hankalin bangarori daban daban.

A cikin rahoton aikin gwamnati, firayin ministan kasar Li Keqiang ya bayyana cewa, kafin karshen shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta cimma burin kubuta daga kangin talauci na duk fadin kasar, tare kuma da tabbatar da zaman al'umma mai matsakaicin karfi a kasar.

Kan wannan, babban sakatare Tuju ya bayyana cewa, ya yi mamaki matuka game da muradun gwamnatin kasar Sin, saboda ba abu ne mai sauki wasu kasashen duniya su cimma irin wannan buri ba, kana yana ganin cewa, sakamakon da kasar Sin ta samar da fasahohi masu ma'ana ga kasashen Afirka na da matukar tasiri, yana mai cewa, "Ina ganin cewa, kasar Kenya tana iya koyon abubuwa da dama daga fasahohin da kasar Sin ta samu, da farko, manufofin da gwamnati take aiwatarwa, da matakan da take dauka suna da muhimmanci. Idan gwamnatin kasarmu ta dauki matakan da suka dace, to kila ne za mu cimma muradunmu, kana ya dace mu koyi kasar Sin wajen tsara salon tafiyar da harkokin kasa, da yaki da cin hanci da rashawa da sauransu."

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya taba bayyana cewa, yayin da ake kokarin dakile annobar COVID-19, ya kamata sassan biyu, wato kasar Sin da kasashen Afirka, su nuna wa juna goyon baya. Ya ce hakika shugabannin kasashen Afirka sama da 50, sun taba aikawa da sako, ko fitar da sanarwa, domin isar da alhini da goyon baya ga kasar Sin, yanzu haka kuma kasar Sin ta riga ta tura tawagoyin kwararrun likitoci da dama zuwa kasashen.

Kan hakan, Tuju ya bayyana cewa, yanayin da ake ciki yayin dakile annobar ya shaida cewa, gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama yana da muhimmanci matuka. Kuma duk da cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar bai yi yawan gaske a nahiyar Afirka ba, amma ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin da kasar Sin ta samu a bangaren yaki da annobar, a cewarsa: "Muna rayuwa a duniya daya, wadda ta kasance gida na daukacin bil Adama, a don haka ina ganin cewa, sanarwar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fitar kan al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama tana da babbar ma'ana. Kasar Sin ta samu rinjaye ta fuskokin ci gaban kimiyya da fasaha, da samar da kayayyakin kiwon lafiya, su kuwa kasashen Afirka, suna morewa matuka, yayin da suke gudanar da hadin gwiwa da kasar Sin."

Hakazalika, gwamnatin kasar Sin ba ta bullo da hakikanin muradunta na karuwar tattalin arziki a bana, bisa dalilin yanayin rashin tabbas da ake ciki, amma Tuju ya nuna imaninsa ga ci gaban tattalin arizkin kasar Sin, ya ce, "Al'ummun kasar Sin ba sa tsoron kalubale, don haka ina cike da imanin cewa, kasar Sin za ta haye wahalhalun da take fuskanta karkashin jagorancin shugaban kasar Xi Jinping, da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, haka kuma Sin za ta kara samun wadata kamar yadda ake fata."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China