Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban daban na yankin Hong Kong sun nuna goyon baya ga daftarin kudurin majalisar NPC kan batun yankin
2020-05-26 11:36:49        cri
Al'ummu daga bangarori daban daban na yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, sun bayyana cewa, an kafa da kyautata tsarin dokoki, da tsarin gudanarwa don kiyaye tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong, da tabbatar da gudanar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" a yankin, wanda ta hakan ne za a tabbatar da zaman lafiya da wadata, da bunkasuwa a yankin.

A jiya ne mataimakin shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC Tung Chee-hwa, ya yi jawabi ta kafar telebijin, inda ya yi bayani kan muhimmancin kafa dokokin a yankin a wannan karo, kana ya yi kira ga jama'ar yankin Hong Kong da su nuna goyon baya ga wannan manufa, don tabbatar da gudanar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" yadda ya kamata.

Tang Ping-keung, wanda shi ne shugaban hukumar 'yan sandan yankin Hong Kong ya bayyana cewa, bisa yanayin tinkarar rikice-rikice da 'yan aware na yankin suke tayarwa sakamakon yunkurin gyara dokokin yankin, 'yan sandan yankin suna fuskantar hadari mafi tsanani na kiyaye tsaron kasa. Ya ce wannan daftarin doka zai taimaka, wajen yaki da 'yan aware na yankin, da inganta odar zamantakewar al'ummar yankin yadda ya kamata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China