Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan NPC suna duba daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a bisa ka'idar martabar al'umma
2020-05-27 13:45:46        cri

A lokacin da suke duba daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a, wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC suna ganin cewa, daftarin ya dace da halin musamman da kasar Sin take ciki, da nuna bukatun al'ummar kasa yadda ya kamata, kamar yadda aka ce, "ana bin ka'idar martabar al'umma bisa dukkan fannonin a lokacin da ake tsara daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a". Ka'idojin dake cikin daftarin suna ba da muhimmanci wajen kare hakkin dan Adam, da inganta wayewar kan al'umma bisa dukkan fannoni.

Babban burin tsara wannan daftari shi ne, kiyaye hakkokin jama'a bisa dukkanin fannoni, babban editan daftarin ya takaita hakkin al'umma daban daban, wadanda suka hada da, hakki kan kayayyaki, kwangila, batun aure da iyalai, batun gado da keta hakki da sauransu, sa'an nan, an tsara dokokin da suka dace wajen kiyaye hakkin jama'a.

Kana, dokar hakkin mutuncin dan Adam dake cikin daftarin ya janyo hankulan al'umma sosai. Wakilin majalisar NPC, kana, shugaban taron abokan hadin gwiwa na kamfanin lauyoyin Hua Ju na lardin Shanxi Liu Zheng ya bayyana cewa, cikin daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a, an jaddada muhimmancin kare mutuncin al'umma, wanda ya nuna ra'ayin martabar al'umma. Ban da dokar mutuncin dan Adam kuma, an kuma hana ta da hankulan jama'a ta hanyoyin buga waya, tura labarai, aika sakwanni da sauransu. Ya ce, dokar ta ba da gudummawa matuka wajen kare sirrin al'umma. Ya ce, "Dokar hakkin mutuncin dan Adam da aka tsara ta dace da bukatun kundin tsarin mulkin kasa na kare mutuncin jama'a, ta nuna amincewarmu kan mutuncin jama'a da kokarin da ake yi domin kiyaye mutuncin jama'a. "

Wakilin majalisar NPC, kana, shugaban kungiyar lauyoyi ta lardin Guangdong Xiao Sheng yana ganin cewa, daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a ya zama takardar sanarwa game da hakkin al'umma. Ya ce, dokar da aka tsara ta fuskar keta hakki, ta yi cikakken bayani kan batun "jefa kaya daga sama", cikin dokar, an tabbatar da nauyin da ya kamata masu kula da gine-gine suka dauka wajen kare tsaron al'umma, domin tabbatar da tsaron jama'a daga faduwar kayayyaki daga sama. Ya ce, "Cikin 'yan shekarun nan, a kan gamu da matsalar jefa kaya daga sama, wadda ya kan halaka rayuwar mutane. Dangane da wannan matsala, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su yi bincike cikin lokaci, domin neman masu aikata laifin jefa kaya daga sama, da mutanen da za su dauki nauyin aikata wannan laifi. Kuma, ya kamata kamfanonin kula da gine-gine su dauki matakan kare tsaro yadda ya kamata. Bayan binciken da aka yi, a kan iya samo mai aikata laifin jefa kaya daga sama, hakan ya sa, ba sai dukkanin mutanen dake zama cikin gini daya sun dauki alhakin aikata wannan laifi ba. Ban da haka kuma, sabo da a tabbatar da nauyin da bangarorin da abin ya shafa za su dauka, kamfanonin kula da gine-gine za su aiwatar da ayyukansu cikin himma da kwazo, ta yadda za a iya kawar da wannan matsala daga tushe."

Haka zalika kuma, an karfafa aikin kiyaye bayanai na yanar gizo, da nuna amincewa kan dukiyoyin yanar gizo a matsayin dukiyoyi, cikin daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a. Wakilin majalisar NPC, kana, shugaban kungiyar lauyoyin birnin Beijing Gao Zicheng yana ganin cewa, wadannan su ne sabbin manufofin da aka bayar ta fuskar sabbin batutuwan dake cikin zaman al'umma. Ya ce, "Daftarin da aka tsara ya dace da halin musamman da muke ciki yanzu, kamar kare tsaron muhimman bayanai na yanar gizo, da kare dukiyoyin yanar gizo da sauransu. Ta yadda za mu sami dokokin da za mu bi wajen kiyaye hakkokin al'umma."

Haka kuma, wakilin majalisar NPC Liu Zheng ya ce, sabuwar bunkasuwar da aka samu cikin sabon zamani, ta kawo sabbin batutuwa ta fuskar dokoki. Cikin wannan daftari, an mai da batutuwan daidaita albarkatu da kare muhalli a matsayin babbar ka'idar dokar da ta shafi harkokin jama'a, lamarin da ya nuna ci gaban da aka samu a fannin tsara dokoki ta fuskar dacewar halin da ake ciki. Ya ce, "An shigar da ra'ayin kare halittu da muhalli cikin daftarin dokar da ya shafi harkokin jama'a, domin batun yana da nasaba da dukkanin al'ummoni, kyautatuwar muhalli zai tallafawa al'umma. Kamar yadda aka tsara cikin dokar kwangila, bangarorin dake kulla da kwangila suna da alhakin daidaita albarkatu da rage kayayyakin gurbata muhalli da za su fitar, wannan ka'ida ta nuna aniyarmu ta kiyaye muhalli." (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China