Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufofin kasar Sin na raya kasa babban darasi ne ga kasashen duniya
2020-05-27 17:52:29        cri

Yanzu haka dai, hankalin duniya ya kartata kan muhimman abubuwan da ake tattaunawa, a manyan taruka biyu na kasar Sin da aka kaddamar, wato taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar ko CPPCC a takaice, da taron majalisar wakilan jama'ar kasar na NPC.

Batun kara rage sassan da a baya aka haramtawa masu jarin waje zuba jari a cikinsu, na daga cikin abubuwan dake kunshe cikin rahoton aikin gwamnati da aka gabatarwa zaman majalisar wakilan jama'ar kasar da aka bude ranar Jumma'a 22 ga wata domin a tattauna a kai. Wannan ya kara bayyana manufar kasar ta kara bude kofa ga waje, duk da yadda annobar COVID-19 ke ci gaba da addabar duniya.

Haka kuma, kasar Sin ta bayyana shirinta na kafa sabbin yankunan cinikayya maras shige na gwaji (FTZs) da yankunan adawa da samar da kayayyaki a yankunan tsakiya da yammacin kasar, da kare tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, baya ga shiga a dama da ita wajen yiwa kungiyar cinikayya ta duniya gyaran fuska.

Rahoton aikin gwamnati da aka gabatar, ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ta jaddada muhimmancin aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya da aka cimma tsakanin Sin da Amurka, wannan ya nuna cewa, kasar Sin abokiyar hadin gwiwa ce, ba ta gaba da kowa.

Sai dai, duk da wadannan matakai da kasar ke fatan aiwatarwa, don bunkasa tattalin arzikinta da ma na duniya baki daya, a bana kasar ta kudiri aniyar kara zage damtse don tabbatar da ganin ta cimma nasarar manufofinta na raya kasa game da kawar da talauci da kammala gina al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni a wannan shekara, duk da cewa, ba ta ayyana wani mizanin ci gaban tattalin arzikin da take fatan cimmawa a shekarar ta 2020 ba, saboda wasu matsaloli na ba zata da kasar ka iya fuskanta yayin da take aiwatar da matakanta na raya kasa, biyo bayan wasu abubuwa na rashin tabbas da ka iya kunno kai dangane da COVID-19, da yanayin tattalin arzikin duniya, da harkokin cinikayya.

Yayin da mahukuntan kasar Sin ke kokarin fito da manufofi da tsare-tsare na raya tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummar Sinawa, a hannu guda kuma hukumomin kasa da kasa na bayyana managartan matakan da kasar ta dauka a fannin yaki da COVID-19 a matsayin babban darasi ga sauran kasashen duniya. Na baya-bayan shi ne, mai magana da yawun asusun ba da lamuni na duniya (IMF) Gerry Rice inda ya bayyana yayin taron manema labarai ta kafar bidiyo, cewar baya ga kwararan matakan da ta dauka don yaki da wannan annoba. Haka kuma kasar Sin tana samun nasara a sauran fannoni, wadanda ka iya zama abin koyi ga sauran kasashen duniya, inda ya bada misali da tsarin biyan kudi na zamani, da cinikayya ta yanar gizo, da hade kananan kamfanoni da kasuwanni da masu sayayya da sauransu.

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin tana da muhimmiyar rawar takawa, wajen taimakawa duniya da kasashe matalauta, musamman alkawarin da kasar ta Sin ta yi, wajen taimakawa shirin rukunin kungiyar kasashen G20 na saukaka biyan bashin da ake bin kasashe masu karamin karfi.

Masu iya magana na cewa, Gani da Ido maganin tambaya. Wannan magana haka take, bisa la'akari da kasancewar kasar Sin wadda a zahiri da ma bayanan masanan lafiya gami da hukumomi na kasa da kasa suka tabbatar cewa, ta zama kasa ta farko a duniya da ta dauki managartan matakai kana ta farko da ta fita daga matsalar cutar COVID-19, a don haka akwai darussa da dama da ragowar kasashen duniya za su iya koya daga gare ta. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China