Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abubuwa masu alaka da jama'ar kasar Sin dake janyo hankalin shugaba Xi
2020-05-28 13:45:54        cri

 


A yau Alhamis, ana kawo karshen tarukan shekara-shekara na majalisun kasar Sin na bana. Sai dai idan an waiwayi lokacin gudanar da tarukan, za mu ga yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna tare da 'yan majalisun kasar Sin, musamman ma kan dabarun da za a dauka don kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar.

Idan an tuna, tun lokacin da aka bude taron wakilan jama'ar kasar Sin a ranar 22 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci tattaunawar da wasu wakilan jama'a na jihar Mongoliya ta gida suka yi, inda a karo da dama ya tambayi wakilan kan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar kan tattalin arzikin jihar.

Hakika tun bayan samun barkewar cutar a kasar Sin, shugaban yana ta kokarin jagorantar aikin kandagarkin cutar, inda ya kira tarukan manyan jami'ai, da rangadi a wurare daban daban har sau 6, gami da musayar ra'ayi tare da manyan kusoshin kasa da kasa har fiye da karo 50. Ma iya cewa, ya san ainihin yanayin da ake ciki na fama da cutar COVID-19 sosai. Amma duk da haka, yayin da yake hira da wakilan da suke wakiltar jama'ar wurare daban daban, ya yi ta sake tambayarsu don sanin yanayin da jama'a suke ciki, kuma ya nanata ra'a yinsa na lura da jama'a:

"Za mu maida jama'a da tsaron rayukansu a gaban kome. Za mu iya sadaukar da duk wani abu, don neman tabbatar da lafiyar jikin jama'ar kasar mu."

Yayin da yake tsara manufofin raya kasa, shugaba Xi Jinping yana dora muhimmanci kan kamfanoni masu zaman kansu, saboda kamfanonin suna taka muhimmiyar rawa a harkokin tattalin arzikin kasar, tare da samar da guraben aikin yi ga mutane kimanin miliyan 300. Yayin da shugaba Xi ke tattauna batun tare da wasu 'yan majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, an ambaci wasu matsalolin da kamfanonin masu zaman kansu ke fuskata, sa'an nan shugaba Xi ya ce:

"Kamfanoni masu zaman kansu sun samu ci gaba sosai a nan kasar Sin. Zuwa yanzu suna samar da gudunmowa sosai ga aikin raya tsarin gurguzu mai salon muamman na kasar Sin. Ya kamata a yi kokarin neman dabaru masu dacewa don daidaita matsalolin da ake fuskanta."

Ban da wannan kuma, shugaban yana maida hankali sosai kan dimbin manoman kasar da suke zama a yankunan karkara. A ganin shugaban, ban da dakile cutar COVID-19, wani aiki na daban mai matukar muhimmanci a shekarar 2020 da muke ciki shi ne kokarin tabbatar da samun nasara a fannin kawar da talauci, gami da ci gaba da zamanintar da fasahar aikin gona. Ya ce,

"Mutane dake cikin zuriyarmu suna da wannan buri, wato dole ne mu yi kokarin taimakawa manoma, don tabbatar da cewa dukkanmu za mu samu wadatar zaman rayuwa."

Ban da wannan kuma, shugaban ya halarci tattaunawar da wakilan jama'ar lardin Hubei suka yi. Wannan lardi shi ne wurin da ya fi fama da cutar COVID-19 a kasar Sin, lamarin da ya sa kasar ta tura kungiyoyin masu aikin likitanci fiye da 340, wadanda ke kunsar kwararrun likitoci da nas-nas fiye da dubu 42 zuwa lardin, don ba da taimako a fannin ceton rayukan mutane. Ta wannan hanya, an samu shawo kan yanayin bazuwar cutar a lardin cikin wasu watanni 3. Yayin da ake zaman majalissar wakilan jama'ar kasar Sin, shugaba Xi ya sanya kulawa kan jama'ar wannan lardi sosai, har ma ya ce dole ne ya ziyarci kungiyar wakilan jama'ar lardin Hubei, inda ya ce:

"Jama'ar lardin Hubei da na birnin Wuhan sun samar da gudunmowa sosai ga aikin dakile cutar COVID-19. Ma iya cewa, birnin Wuhan wani birni ne na jarumai. Ina so in nuna jinjina da godiya ga al'ummar lardin."

Sa'an nan shugaban ya kara jaddada bukatar daidaita tsarin kandagarkin cututtuka, da kyautata tsarin aiki na yin gargadi ga jama'a kan bullar wata cuta, gami da gudanar ayyuka na wayar da kan jama'a dangane da ilimi mai alaka da kiwon lafiya da kandagarkin cuta, da dai makamantansu.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China