Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tallafin Sin ga Namibia yana zurfafa cudanyar sassan biyu musamman a gabar da ake yaki da COVID-19
2020-05-28 18:31:27        cri

 

A baya bayan nan, tallafin da kasar Sin ke samarwa kasashen Afirka a fannin yaki da annobar COVID-19 na karuwa, wanda hakan ya shaida alkawarin da Sin din ta jima da yi, na taimakawa aminan ta na Afirka, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, kuma gwargwadon karfin ta.

Baya ga tallafin kayayyakin kariya, da na kandagarkin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da ma kayan gwajin cutar domin dakile yaduwar ta, wadanda suka isa nahiyar a karo daban daban, karkashin gidauniyar hamshakin dan kasuwar nan na kasar Sin Jack Ma, da gidauniyar Alibaba, su ma kamfanoni masu zaman kan su, da kungiyoyin 'yan kasuwar Sin, da wakilan kamfanonin Sin dake aiki a Afirka, da ma ofisoshin jakadancin Sin dake nahiyar, suma sun bi sahu, wajen tallafawa yankunan nahiyar daban daban.

A kasar Namibia, irin wannan tallafi daga kafofi masu zaman kan su, domin tallafawa yaki da ake yi da wannan annoba na kara fadada, yana kuma kara shaida cika alkawarin da Sin ta jima tana yi, na ci gaba da bunkasa alakar Sin da al'ummar Namibia.

Misali a kan hakan shi ne, yadda a baya bayan nan ofishin jakadancin Sin dake Namibia, da kungiyar Sinawa mazauna kasar suka samar da tallafin kayayyakin masarufi ga mutane 230, a kauyen Shighuru dake yankin Mashare wanda ke karkashin jihar Kavango ta gabashin kasar.

 

Kayayyakin da mazauna kauyen Shighuru suka samu sun hada da na yaki da karancin abinci, sakamakon bullar cutar COVID-19 a sassan kasar.

Yayin mika tallafin, 'yar kasuwa Basiniya Charlene Chen, ta ce mutane mazauna yankunan karkara na cikin wadanda wannan anoba ta shafa, kuma burin bangaren Sin shi ne taimakawa wadanda ke cikin matsananciyar bukata, musamman a wannan lokaci da ake da matukar bukatar inganta lafiyar jikin al'umma. Ta ce "Ta haka ne za mu iya gina kyakkyawar dangantaka tsakanin mu".

Irin wannan taimako yana samun matukar karbuwa ga al'ummun Afirka, kasancewar sa taimako da ba ya kunshe da wani sharadi. Kaza lika taimako ne da kasashen Afirka ke karba, a gabar da kasashen nahiyar ke matukar bukatar sa.

Ko shakka ba bu, tallafin na Sin ga Namibia, yana da tasirin gaske wajen sake dinke alakar kasashen biyu, yana kuma tabbatar da al'adar gargajiya ta Sin, ta tausayawa, da kuma taimakawa kawayen ta a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Game da wannan tallafi na baya bayan nan, jakadan Sin a Namibia Zhang Yiming, ya ce kasar sa za ta ci gaba da mara baya ga 'yan uwan su na Namibia, a yakin da kasar ke yi da cutar COVID-19.

 

 

Kalaman na jakada Zhang dai na zuwa a gabar da al'ummar Namibia ke kara rungumar salon jiyyar gargajiyar kasar Sin, ciki hadda amfani da allurai domin magani, inda a yanzu haka, 'yan kasar ke halartar asibitin gwamnati dake Katutura, domin a yi musu magani da allurai bisa fasahar likitanci ta kasar.

Dukkanin wadannan matakai na Sin, na tallafawa Namibia da kayayyakin kiwon lafiya, da gabatar da dabarun kiwon lafiya da jinya irin na kasar Sin, alamu ne dake nuna karfin dandantaka tsakanin kasashen biyu, da kuma yaukakar zumunci tsakanin sassan, tare da fatan ci gaba da fadada alakar Sin da Namibia, da ma sauran sassan nahiyar Afirka baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China