Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan shari'a: Kundin dokar zamantakewar al'umma ta dace da muradun jama'ar kasar Sin
2020-05-29 14:32:07        cri

Taro na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na 13 ya zartas da kundin dokar zamantakewar al'umma na farko a kasar Sin a yammancin jiya Alhamis, za a fara gudanar da wannan doka daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar dake tafe. Karo na farko ne aka kafa wata doka da sunan kundin doka, kuma ita ce shari'a dake kunshe da ayoyi mafi yawa a kasar Sin. A ganin wasu masana a fannin shari'a da doka, wannan doka za ta ba da cikakken tabbaci ga tsarin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje da kuma aikin zamanintar da al'ummar Sinawa.

Wannan kundin dokar na kunshe da babi 7 masu ayoyi 1260, wato takaitaccen bayani, ikon mallakar abubuwa, kwangila, da hakkin da ake da shi bisa matsayi na mutum, da kuma aure da iyalai kana da ikon gadon dukiyoyi da kuma ayyukan keta hakki da kuma karin wasu bayanai.

Daga cikinsu, an ware hakkin da ake samu bisa matsayi na mutum ya zama wani babi mai zaman kansa, wanda ke da ma'ana sosai. Wakilin NPC kuma mambar kwamitin shari'a da doka na NPC wanda ya shiga aikin tsara wannan kundi mista Sun Xianzhong ya ce:  

"An mai da hakkin da ya zama wani babi mai zaman kansa a cikin kundin doka, bisa tanade-tanade na aya ta 109 dake cikin dokar zamantakewar al'umma, don bada tabbaci ga hakkin mutum da kuma mutuncin jama'a da kara kiyaye 'yancin jama'a, ta yadda za a kiyaye hakkin jama'a na neman biyan bukatunsu a fannin hankali."

Zaunannen dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa kana mataimakin shugaban babban kotun kasar Sin Li Shaoping ya ce, wannan mataki ya bayyana cewa, kundin doka na mai da hankali sosai kan jama'a don kiyaye hakkinsu. Ya ce:

"Kafin wannan dai, hali da kuma mutumcin jama'a wani tsari ne kawai a cikin tunanin harkokin jama'a. Amma a wannan karo an maida shi wani babi a cikin kundin doka, abin da ya bayyana cewa dokar tana maida hankali kan kiyaye hakkin jama'a."

A matsayin wani masani a fannin dokar zamantakewar jama'a, Sun Xianzhong ya ce, kowane mutum zai ci gajiyar wannan doka, kuma dokar za ta ba shi kariya a duk tsawon rayuwarsa.

Dokar zata baiwa jama'a tsaro, kuma za ta maida hankali kan nauyin dake wuyan jama'a. Li Shaoping ya bayyana cewa:

"Ba ma kawai muna kokarin daidaita dokar harkokin jama'a don ta zama wata doka mai cike da inganci ,dake dacewa da zamani ba ne, har ma zata bayyana hakikanan matakan da za a dauka wajen warware matsalolin da jama'a suke fuskanta. Alal misali, yadda za a warware matsalar jefa abubuwa daga saman wani gini mai tsayi. An hana yin wannan abu a cikin kundin doka, kuma wadanda suka yi hakan za su dauki nauyi."

Tun kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, an gudanar da aikin tsaida doka da shari'a kan zamantakewar al'umma sau 4. Tsaida wani kundin doka dake dacewa da muradun jama'a buri ne na Sinawan zuriyoyi daban daban, sai dai ba a cimma wannan buri ba cikin wani dogon lokaci.

Tun babban taro karo na 18 na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, jam'iyyar ta mai da hankali matuka kan gudanar da harkokin kasar bisa doka da shari'a, a gun cikakken zama na 4 na babban taro karo na 18 na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin an gabatar da wannan babban aiki, an kuma kwashe shekaru 5 ana kokarin tsaida wannan kundin doka.

A ganin Sun Xianzhong, fitowar wannnan kundin doka akwai ma'ana sosai ga zamanintar da tsari da kuma samun karfin gudanar da harkokin kasar. Ya ce, muhimmin abu dake cikin wannan kundin doka shi ne jama'a su dogaro da kansu don aiwatar da wannan doka. Doka dai ta ba da jagoranci da kuma tabbaci ga jama'a a wannan fanni.

Ban da wannan kuma, Sun Xianzhong ya ce, wannan kundin doka ba wata sabuwar doka ba ce, amma ta dace da halin da ake ciki yanzu. Alal misali, a baya-bayan nan an sha mai da hankali kan dukiyoyi a cikin zaman rayuwa, amma yanzu ban da wadannan dukiyoyin, ana da dukiyoyi a kan Intanet wato hannayen jari da dai sauransu. Don haka, kundin doka a wannan karo ya mai da hankali sosai kan wadannan dokiyoyi. Ban da wannan kuma dokar ta bayyana halaye na zaman al'umma na wannan zamanin da muke ciki, wannan wani sabon salo ne da ba a taba ganin irinsa cikin dokokin kasashe daban daban ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China