Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren harkokin wajen Amurka da bai tabuka komai ba yana sanya kasar cikin mawuyacin hali
2020-05-29 20:24:26        cri

"Shi ne sakataren harkokin waje da bai tabuka komai ba, wanda kuma ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar Amurka, bai cimma duk wata nasara a harkokin siyasa ba." Wannan ne yadda tashar intanet ta jaridar "The New York Times" ta bayyana sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, a cikin zargin da ta yi masa a sharhin da ta wallafa.

Wannan ya nuna cewa, bisa tsanantar yanayin annobar COVID-19 da kasar ke ciki, al'ummar kasar na kara fahimtar hasarar da Pompeo ke jawo wa rayuwar jama'a da ma moriyar kasar.

A cikin sharhin, an tona yadda Pompeo bai tabuka komai ba a fannin harkokin waje, da tayar da rade-radi, da dora alhaki ga saura, da kuma amfani da albarkatun tarayyar kasar ba bisa doka ba da dai sauransu. Ga misalin, sharhin ya nuna cewa, Pompeo ya yada maganar makirci game da asalin cutar COVID-19, kana kuma domin cimma burinsa na kara ci gaba a hanyarsa ta siyasa. Bayan ya bukaci ma'aikatan gwamnati su kula da harkokinsa, da amfani da kudin gwamnati don shirya bikin liyafar dare, ya kuma yi amfani da albarkatun tarayyar kasar don horar da magoya bayansa da dai sauransu.

Lallai, har zuwa yanzu dai babu wani sakataren harkokin waje da halinsa ya yi kama da na Pompeo ba a tarihin Amurka, inda tuni ya riga ya bata sunansa a cikin kasar ta Amurka da ma kasashen ketare. "Bai tabuka komai ba". Irin kimantawa da aka yi masa ya tantance halinsa sosai. A wani bangare, Pompeo ya samu amincewa daga wajen shugabansa ta hanyar yi masa bambadanci, a waje guda kuma yana samun moriya sakamakon amfani da amanar shugabansa.

Ban da wannan kuma, Pompoe yana ta tayar yanayin yada jita-jita a kasashen duniya, don shiga tsakani da tayar da gaba, duka sun nuna karancin matsayin da'arsa.

Daga bata sunan kasar Sin zuwa haifar da barazana ga kawancen kasarsa, gaskiya Pompoe yayi namijin kokari a kai. A idanunsa, babu kawance, sai dai kayayyakin da yake amfana don neman moriyar siyasa, ko kuma wadanda ke raka su wajen tayar da rade-radi, ko kuma kayayyakin sadaukarwa da yake amfani da su wajen matsawa kasar Sin lamba. Kamar yadda tsohon shugaban majalisar Turai Donald Tusk ya fada: Duk wata kasa da ta zama abokiyar Amurka, ta riga ta samu abokiyar gaba.

Yanzu, mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon annobar COVID-19 sun wuce dubu 100 a kasar Amurka, amma duk da haka, Pompeo na ci gaba da shigar da kasar cikin mawuyacin hali. Ko wannan 'dan siyasa wanda kullum ke cewa yana "girmama tsoron Allah" amma ba ya tsoron Allah za a yanke masa hukunci? (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China