Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Sinawa suka isa tsororuwar tsaunin Qomolangma ya shaida matukar kokarin al'ummar Sin wajen cimma buri ba tare da tsoron komai ba
2020-05-31 17:27:25        cri

Da karfe 11 na safiyar ranar 27 ga watan Mayun bana, mambobi 8 na kungiyar masu hawa tsauni na kasar Sin sun isa tsororuwar tsaunin Qomolangma, wanda shi ne tsauni mafi tsayi a duniyarmu, inda suka dasa tutar kasar Sin da kuma fara gudanar da ayyukan safiyo iri daban daban. Wani abin ban al'ajabi shi ne, lamarin ya zo ne a makamanciyar wannan ranar a shekarar 1975, Sinawa sun taba kai tsororuwar tsaunin, wanda ya kasance karo na farko ga dukkanin bil Adama, sa'an nan sun sanar da cewa, tsaunin yana da tsororuwar tudun mita 8,848.13.

A wannan karo, bayan kwashe kusan watan guda, a karshe dai kungiyar masu hawa tsauni ta Sin ta sake isa tsororuwar tsauni mafi tsayi na duniya, lamarin da ya jawo hankulan duniya baki daya. Haka kuma ba kawai lamarin ya kasancewa wata sabuwar ishara a tarihin hawa tsaunuka na Sin ba ne, hatta ma yana da babbar ma'ana ga aikin hawa tsaunaka na duniya, ganin yadda ya shaida kyakkyawar hallayar al'ummar Sin.

Da farko dai, hawan tsaunin Qomolangma ya nuna karfin kasar Sin wajen kirkire-kirkire. Yayin da mambobin kungiyar ke hawan tsaunin, sun yi amfani da na'urar GNSS da ma tauraron dan Adam na Beidou wajen tabbatar da inda suke ciki, kana sun yi amfani da na'urar tsarin radar wajen auna tsayin dusar kankara dake tsororuwar tsaunin, da ma amfani da wata na'urar musamman wajen auna karfin maganadisun kasa, wanda ya kasance karon farko da dan Adam ya yi hakan a kolin tsaunin Qomolangma. Dukkan wadannan na'urorin aikin safiyo kasar Sin ne ta kirkira da kanta, wadanda ake sa ran za su taimaka wajen samun kididdigar kimiyya mai matukar daraja da ma tantance tsayin tsaunin tare da kaucewa duk wani kuskure, ta yadda za a fadada ilimin bil Adama game da yanayin halittun duniya da kuma bunkasa ci gaban binciken kimiyya, baya ga kara fahimtar kwarewar kasar Sin a fannin kimiyya da fasaha.

Na biyu, hawan tsaunin Qomolangma ya shaida karfin hadin gwiwar al'ummar kasar Sin. Tun bayan da mambobi uku na kungiyar hawa tsaunuka ta Sin suka isa tsororuwar tsaunin Qomolangma a shekarar 1960, kasar ba ta taba dakatar da aikin hawan tsaunukan don binciken halitta da ma kokarin kai iyakar bil Adama ba. A cikin aikin hawan tsaunin da aikin safiyo na wannan karo, ba ma kawai jarumtakar da mambobin kungiyar suka nuna ta burge mu sosai ba ne, har ma muna iya jin babban karfin hadin gwiwar sassa daban daban yayin da suke kokarin hawan tsaunin, ganin yadda sassa masu kula da yanayi, sadarwa, likitanci, hidimomi suka yi hadin kai sosai domin taimakawa masu hawan tsaunin sun cimma burin.

ba su dakatar da aikinsu ba. Yadda suka cimma wannan babban burin a wannan mawuyacin halin da ake ciki, ya zubawa duk al'ummar Sin babban karfi wajen tinkarar cutar, lallai yana da babbar ma'ana ta musamman.

Komen tsayin tsauni, kada a ji tsoro, sai a yi kokarin hawansa. Yadda kasar Sin ta kokarta don kai tsororuwar tsaunin Qomolangma wani abin shaida ne na himmatuwar Sinawa ba tare da kasala ba tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949. Muddin akwai niyya da ma ruhi mai karfi, komai tsayin tsaunin, za a iya kai tsororuwarsa, komai wahalar da ake gamuwa da ita, za a iya hayewa.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China