Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Burtaniya: Ana iya koyon fasahohin Sin na kawar da talauci
2020-06-01 13:54:28        cri

Shugaban cibiyar kasar Sin ta jami'ar Oxford, kana masanin tarihi da siyasa na kasar Sin, Rana Mitter ya yi tsokaci kan tarukan majalissu biyu da aka kammala kwanan baya a kasar Sin. Mr. Mitter ya ce, manufofi da fasahohin na kasar Sin game da kawar da talauci sun zama abin koyi ga kasa da kasa, kuma manufofin dake shafar tattalin arziki da kasar Sin ta fito da su a yayin tarukan biyu na bana, sun janyo hankulan kasa da kasa. Yana ganin cewa, annobar cutar numfashi ta COVID-19 za ta sa kaimi ga kasar Sin wajen raya ingantaccen tattalin arziki, ta yadda za ta hada bunkasuwar kimiyya da fasaha da tattalin arziki tare.

Rana Mitter ya ce, shekarar 2020 ta kasance muhimmiyar shekara ga kasar Sin ta fuskar kawar da talauci baki daya a kasar Sin. Kuma bisa manufofin taimaka wa masu fama da talauci da aka tsara a yayin tarukan majalissun biyu, a mataki na gaba, Sin za ta mai da hankali wajen daidaita matsalar rashin daidaito tsakanin yankuna daban daban na kasar. Ya ce, "Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, za ta gyara manufofin raya kasa, musamman ma a yankuna masu fama da talauci, da yankunan dake yammacin kasar, kamar lardin Gansu, da wuraren da ba su da bunkasuwar tattalin arziki. Shi ya sa, a ganina, babban kalubalen dake gaban kasar Sin ta fuskar kawar da talauci shi ne, daidaita matsalar rashin daidaito tsakanin yankuna daban daban na kasar, wannan zai zama buri na gaba ta fuskar kawar da talauci."

Ya yi karin bayani cewa, ana iya koyon fasahohin kasar Sin wajen kawar da talauci, ciki har da wasu fasahohin da kasashe masu ci gaba za su iya koyo daga wajenta. Yana mai cewa, "Kasashe da dama suna iya koyon fasahohin kasar Sin domin neman ci gaba, daya daga cikin wadannan fasahohi shi ne, kafa yankin musamman na tattalin arziki na gwaji. Kasar Sin ta fara wannan aiki daga shekaru 1980, a zamanin mulkin Deng Xiaoping. Ban da haka kuma, wata muhimmiyar fasaha ta daban ita ce, zuba jari a harkokin kimiyya da fasaha da gina ababen more rayuwa. Akwai dalilai da dama da suka tabbatar da bunkasuwar kimiyya da fasaha a kasar Sin, har ta zama jagora a wannan fanni a duniya, kuma daya daga cikin wadannan dalilai shi ne, ci gaba da zuba jari, kuma mai yawa a aikin nazari da raya kimiyya da fasaha. Wadannan fasahohi za su iya zama abin koyi ga kasashe masu ci gaba, sabo da wasu ba sa zuba isassun jari a aikin nazari, da habaka kimiyya da fasaha."

Haka kuma, ya ce, yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin a bana ta haddasa hasara ta gajeren lokaci ga tattalin arzikin Sin. A sa'i daya kuma, ta kawo wasu damammaki ga kasar, biyo bayan kwaskwarimar da kasar Sin ta yi a wannan fanni cikin 'yan shekarun nan. Kasar Sin ta kasance kasar dake kan gaba wajen raya harkokin kasuwanci ta yanar gizo, kuma yaduwar annobar ta canja hanyoyin sayayyar al'ummar kasa. Ya ce, "Abin sha'awa shi ne, yaduwar annobar ta canja hanyoyin musayar tattalin arziki tsakanin al'umma. Zan ba da misali da kasuwanci ta yanar gizo. Mun san cewa, akwai kamfanonin kasuwanci ta yanar gizo da dama a kasar Sin, kamar kamfanin Alibaba da kamfanin Tencent da sauransu. Abin dake janyo hankalina shi ne, a lokacin annobar, Sinawa sun fi son yin sayayya ta yanar gizo, a ganina, za a iya ci gaba da wannan harka, saboda tana da sauki ga kuma damammaki a ciki. Tabbas wannan fanni zai ci gaba matuka."

Bugu da kari, Rana Mitter ya ce, cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta kara mai da hankali kan raya tattalin arziki mai inganci, musamman ma a fannin kimiyya da fasaha. Annobar ba ta haddasa babbar hasara kan wannan aiki ba, kuma a nan gaba, kimiyya da fasaha da tattalin arziki za su bunkasa baki daya. Ya ce, "A nan, mun fito da wani muhimmin batu, wato bunkasuwar tattalin arziki. A ganina, yadda ake yin sayayya ya zama wani muhimmin batu dake sa kaimi ga bunkasuwar kimiyya da fasahar kasar Sin. Idan muka duba hanyar biyan kudade, za a ga cewa, al'ummomin Sin suna amfani da wayar salula a maimakon tsabar kudi wajen biyan kudi. Shi ya sa, 'yan kasuwa za su kara fahimtar yadda mutanen suke sayayya ta hanyar nazarin muhimman bayanansu. Bayan annobar, za a zurfafa hade kimiyya da fasaha da harkokin kasuwanci waje guda. Sabo da haka, mai da hankali kan raya tattalin arziki mai inganci, zai kasance wata muhimmiyar dama, kuma yanayin tattalin arziki da ya sauya sakamakon yaduwar annobar zai gaggauta wannan aiki." (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China