Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ficewar Amurka daga WHO gurguwar shawara ce
2020-06-01 19:38:33        cri
Masu iya magana na cewa da walakin wai goro a miya. Tun lokacin da shugaba Trump na Amurka ya yi barazanar dakatar da kason kudaden da kasarsa take baiwa hukumar WHO, masana suka fara hasashen dama inda kasar ta dosa ke nan dama neman katse hulda take yi da hukumar. amma ta ki fitowa fili ta bayyanawa duniya nufinta abin da masu iya magana ke cewa, dama za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Wannan mataki na gwamnatin Amurka batu ne da ya gamu da mummunan suka daga kasashen duniya. Idan har Amurka tana tunanin wannan shi ne waraka a wajenta to ai tamkar an kashe maciji ne amma ba'a sare kan ba, domin kuwa wannan mataki ne da ita kanta zai shafi moriyarta.

Koda yake, da ma dai matakin bai zo da mamaki ba, kasancewar shugaban Trump tun a ranar 18 ga watan Mayu ya rubutawa babban darektan hukumar lafiya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus wasika, inda ya yi barazanar cewa muddin hukumar WHO ta gaza yin wasu sauye sauye cikin kwanaki 30 daga wancan lokacin, to ba shakka Amurka za ta dakatar da biyan kudaden mamba ga hukumar, sannan za ta karkatar da akalar kudaden da take baiwa hukumar zuwa wasu fannoni na daban, sannan ya ce Amurkar za ta sake yin nazarin ko za ta ci gaba da kasancewa mamba a WHO ko akasin haka, yanzu dai baki alkalami ya riga ya bushe tun da Amurka ta sanar da matsayinta a daidai lokacin da duniya ke bukatar hadin gwiwa don ganin bayan cutar COVID-19 da ma sauran harkokin lafiya da suka shafi daukacin duniya. Har yanzu dai Amurka ba ta makara ba tana iya canza ra'ayinta domin dawowa cikin dangi.

Sai dai a yayin da Amurka ke daukar wannan mataki, a hannu guda kuma, wasu manyan jami'an kungiyar tarayyar Turai EU da kasashen Iran da Rasha suna yiwa Amurkar hannunka mai sanda kan bukatar ta sake tunani kan kudirin da ta dauka na yanke alaka da hukumar ta WHO, domin hakan ba zai haifar mata da da mai ido ba, amma masu iya Magana na cewa mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.

A yayin da duniya ke fama da wannan mummunan kalubale, yanzu lokaci ne da ya dace a hada gwiwa domin neman mafita tare a maimakon nuna bukatar kashin kai, tilas ne a kaucewa daukar dukkan wasu matakai da za su iya kawowa kasa da kasa mummunan sakamako a wannan mawuyacin hali na yaki da annobar COVID-19, gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China