Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasar Amurka da suka tayar da tarzoma a HK suna shan wahalar da suka haifar
2020-06-01 20:59:50        cri

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wani mutum 'dan asalin Afirka, ya mutu a sanadin kisan gillar da wasu 'yan sanda farar fata a jihar Minnesota ta kasar Amurka suka yi masa, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a kai a kai, a biranen kasar sama da 70, har ta kai ga samun hargitsi tare kuma da lalata kantuna a wasu sassan kasar. An lura cewa, irin wannan lamari ya taba faruwa a Hong Kong, wanda yankin musamman ne na kasar Sin.

Amma abun mamaki shi ne, 'yan siyasar Amurka sun manta da cewa, sun taba ayyana masu tayar da tarzoma a titunan Hong Kong a matsayin "sojojin shimfida demokuradiyya", kana kuma sun manta sun taba zargin 'yan sanda wadanda suke tabbatar da tsaron mazauna yankin, sai ga shi a yanzu haka suna kiran zanga-zangar da ake yi a wurare daban daban na Amurka a matsayin "hargitsi", suna kiran fararen hular kasar wadanda ke yin adawa da wariyar launin fata a matsayin "masu tayar da zaune tsaye", suna kuma yabawa 'yan sanda wadanda suka cikin mota domin yin fito-na-fito da masu zanga-zanga, har ma suka kashedin cewa, za su bude wuta kai tsaye, ko kuma sojojin kasar za su dauki mataki.

Hakika ma'auni iri biyu da 'yan siyasar Amurka suke amfani da shi ya nuna wa al'ummun kasashen duniya cewa, wadannan 'yan siyasar ba sa kulawa da adalci da doka ko kadan, maimakon haka suna kulawa ne kadai da takardun zabe da moriyar siyasa.

Kafofin watsa labaran Hong Kong sun fayyace cewa, tun daga shekarar 1995, har zuwa farkon shekarar 2015, gaba daya, adadin kudin tallafin da asusun demokuradiyyar kasar Amurka, wanda aka kafa bisa dokar majalisar dokokin Amurka ya samar wa masu yin adawa da gwamnatin yankin Hong Kong, ya kai sama da dalar Amurka miliyan 3 da dubu 950. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, manyan jami'an Amurka, kamar su mataimakin shugaban kasar Mike Pence, da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, da shugabar majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi, da sauransu, sun yi ganawa da madugun masu tayar da tarzoma a yankin HK sau da dama, kana 'dan majalisar dattijan kasar Marco Rubio, yana ta tsara dokar hakkin dan Adam da demokuradiyya ta Hong Kong, ta shekarar 2019, domin nuna goyon baya ga masu tayar da hargitsi a yankin.

Wanda ke lalata saura zai lalata kansa. Ana sa ran cewa, 'yan siyasar Amurka za su daina daukan matakan da ba su dace ba. Ya dace su daidaita hargitsin da ya faru a cikin kasarsu tun da wur wuri. Ko shakka babu gwamnatin kasar Sin za ta nacewa manufarta ta kiyaye 'yancinta, tare kuma da cimma burin raya kasa cikin lumana. Haka kuma za ta nacewa manufarta ta "kasa daya mai tsarin mulki biyu", kuma ba zai yiwu ta amince da kasashen waje su tsoma baki a cikin harkokin Hong Kong ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China