Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a bude kakar La Liga ta 2020 zuwa 2021 a watan Satumba
2020-06-04 16:37:21        cri

Shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya Javier Tebas, ya ce za a bude kakar kwallon kafar kasar ajin kwararru ta La Liga ta 2020 zuwa 2021 a ranar 12 ga watan Satumba, bayan kallama kakar 2019 zuwa 2020 nan da karshen watan Yuli.

Da yake tsokaci yayin zantawa da masu ruwa da tsaki ta kafar bidiyo, Tebas ya ce yana fatan za a kai ga fara buga sauran wasannin La Liga 11 da suka rage, a wannan kaka tun daga ranar 11 ga watan Yuni, ko da kuwa ta hanyar buga wasa daya a duk rana ne, yayin da kuma kungoyoyi za su rika buga wasa bayan sa'oi 72, domin cimma burin kammala kakar cikin sauri.

Mr. Tebas ya kara da cewa, "Akwai mutane 130 a tsarin gasar La Liga da ke aiki ba dare ba rana domin tabbatar da nasarar hakan; suna kuma tafiye tafiye, da tsara ayyuka, da sauran abubuwa.

Ya ce da yake an tsara buga gasar wasannin turai a cikin watan Agusta, ke nan dole a fara kakar wasanni mai zuwa da wuri fiye da yadda aka yi tsammani a baya. Bugu da kari, sauran wasannin kakar da ake ciki za a buga su ne ba tare da 'yan kallo ba. Amma bai bayyana yaya za ta kasance a sabuwar kakar wasannin da za ta biyo baya ba. Ko da yake dai ya tabo batun muhimmancin bangaren tattalin arziki na gasar kwallon kafar kasar ta Sifaniya. Ya ce "Mun tara kudade da yawan su ya kai kaso 1.37 bisa dari na GDPn kasar Sifaniya, mun kuma samar da guraben ayyukan yi har 185,000," .

An baiwa kungiyoyin Serie A na Italiya damar ci gaba da taka leda karkashin dokokin dakile cutar COVID-19

Tun bayan dakatar da taka leda kimanin makwanni 12 da suka gabata, bayan da kungiyoyin kwallon kafar Italiya ajin kwararru ko Serie A suka shiga zaman gida, yanzu haka gwamnatin kasar ta baiwa hukumar kwallon kafar kasar damar sake bude wasanni tun daga ranar 20 ga watan Yuni.

Ministan wasannin kasar Vincenzo Spadafora ne ya sanar da matsayar kasar, bayan kammala wani taro na kasa da sa'a daya ta kafar bidiyo, tare da wakilan hukumar kwallon kafar ta Italiya, da mashirya gasar ta Serie A, da 'yan wasa, da masu horas da 'yan wasa, da alkalan wasan. Hakan dai na zuwa ne bayan shafe tsawon makwanni kafafen watsa labarai na ta cece-kuce, da hasashe game da matakin da gwamnatin za ta dauka.

A farkon watan nan, kungiyoyi 16 cikin 20 dake buga gasar Serie A, sun amince da a sake komawa taka leda, tun daga ranar 13 ga watan Yuni, inda kungiyoyi 4 suka amince a koma wasannin daga ranar 20 ga watan Yuni. To sai dai duk da an amince a koma wasanni, a hannu guda an bukaci kungiyoyin da za su taka leda, da su kiyaye wasu ka'idoji na kiyaye lafiya, da tsaron 'yan wasa.

Bisa amincewa da wannan ka'ida, 'yan wasa za su rika taka leda ba tare da 'yan kallo ba, za kuma a rika yiwa 'yan wasa da jami'ai gwajin cutar COVID-19. An tsara cewa, idan aka samu wani dan wasa dauke da wannan cuta, to za a killace dukkanin wadanda ya yi cudanya da su.

Sauran kungiyoyin kwallon kafa dake taka leda a sauran azuzuwan kwararru na kasar, ciki hadda masu buga Serie B da Serie C, da kuma ajin mata masu buga Serie A, su ma za su koma buga wasanni nan gaba kadan.

Kafar watsa labaran wasanni ta Spadafora, ta yi kashedin cewa, idan alkaluman yawan masu dauke da cutar coronavirus suka karu a Italiya, bayan kyautatuwar yanayi tun daga tsakiyar watan Afirilu, akwai yiwuwar a sake dakatar da buga wasannin.

An tsayar da ranar 17 ga watan Yuni a matsayin ranar da mai yiwuwa a koma Firimiyar kasar Ingila.

Mahuntan kwallon kafar kasar Ingila, sun sanar da tsayar da ranar 17 ga watan Yunin nan, a matsayin ranar da mai yiwuwa za a koma taka leda a gasar Firimiyar kasar Ingila.

Wata sanarwa da aka fitar a ran Alhamis din makon jiya, ta ce "Masu ruwa da tsaki a gasar ta Firimiya, sun amince da ranar da aka sanya, domin kammala kakar wasa ta shekarar 2019 zuwa 2020, muddin dai an tanaji dukkanin matakai na ba da kariya yadda ya dace."

Shugaban hukumar gudanarwar gasar Firimiyar kasar ta Ingila Richard Masters, ya tabbatar da cewa, "Ba za a kai ga tabbatar da wannan rana ta bude taka leda ba, har sai an fayyace dukkanin tanajin matakan tsaron lafiya, yayin da jami'an tsaro da ma'aikatar kula da walwalar jama'a ke shiga a dama da su, wajen inganta matakan da za a bukata, na kare lafiyar kowa".

An dai dage dukkanin wasannin Firimiya, da sauran gasanni da ake bugawa a Ingila, tun daga ranar 13 ga watan Maris, sakamakon barkewar cutar COVID-19. An dai amince manyan kungiyoyin kasar 20 su koma wasanni cikin kananan rukunoni, tare da kiyaye cakuduwa tsakanin 'yan wasa a yayin gudanar da atisaye tun daga ranar Talatar da ta gabata, daga bisani kuma aka amince a yi atisaye tare da cudanya tsakanin 'yan wasan tun daga ranar Laraba.

Yanzu haka dai akwai ragowar wasannin Firimiya 92, na kakar wasanni da ba a kammala ba, wadanda kuma yanzu haka ake fatan nuna su ta kafofin watsa shirye shirye kai tsaye daga kasar ta Ingila.

Mr Masters ya ce "Abun takaici ne, ganin yadda wasanni za su rika wakana ba tare da 'yan kallo ba, don haka muka tanaji dabarun tabbatar da cewa, 'yan kallo sun samu damar ganin ragowar wasannin 92 kai tsaye ba tare da wata matsala ba. Masters ya kara da cewa, "Abu ne mai matukar muhimmanci, jama'a su samu damar kallon wasannin ba tare da wata matsala ba."

Kafar Sky sports, wadda ke da ikon nuna wasannin gasar Firimiya 64 kai tsaye, ta alkawarta nuna wasanni 25 kyauta.

A ranar Larabar da ta gabata, hukumar Firimiya ta tabbatar da samun karin sabbin mutane 4, wadanda suka harbu da COVID-19, wanda hakan ya daga alkaluman masu dauke da cutar zuwa mutum 12, cikin wadanda ke buga gasar, bayan da aka yi gwajin mutane 2,752 a zagaye 3.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China