Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar ma'aikatan jinya ta kasar Sin mai taimakon Equatorial Guinea ta kammala aikinta yadda ya kamata
2020-06-08 13:52:43        cri

Yau Litinin agogon kasar Equatorial Guinea, tawagar ma'aikatan jiyya ta kasar Sin mai taimakon kasar, ta kammala aikinta yadda ya kamata, inda za ta dawo gida. Yayin da masanan ke tallafawa kasar, su kan yi rangadi a asibitocin wurin da dakunan gwaje-gwaje na kasar da sauran wurare, don koyar da su dabaru da fasahohin kasar Sin a fannin yakar COVID-19. Firaministan kasar Francisco Pascual Obama Asue ya yaba tawagar, yana mai cewa, ta baiwa kasar haske wajen yakar wannan mumunar cutar.

Equatorial Guinea tana yamma maso tsakiyar nahiyar Afrika. A halin yanzu, COVID 19 na yaduwa a duniya, wannan kasa dake da yawan mutane miliyan 1.3 ta tabbatar da mutane fiye da 1300 da suka kamu da cutar. Dadaren ran 25 ga watan Mayu, tawagar kasar Sin ta isa kasar, don taimaka mata kandagarkin cutar. Wannan tawaga mai masana 12 a fannonin kula da lafiyar numfashi da yaki da annoba da cututuka masu tsanani da ba da kulawa. Kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin ne ya kafa tawagar, shi kuma kwamitin kiwo lafiya na lardin Hunan ya tura ta zuwa kasar.

Shugaban tawagar kana mataimakin darektan kwamitin kiwo lafiya na lardin Hunan Zhu Yimin ya bayyana cewa, tawagar ta ba da horo da shawarwari bisa halin da ake ciki a kasar. Ya ce,

"Mun kai rangadi wasu asibitoci da aka kebe a matsayin asibitoci masu kula da COVID 19 a Malabo hedkwatar kasar da kuma asibitocin dake kula da annoba, ciki hadda asibitocin kasar da kuma masu zaman kansu, da kuma dakunan gwaje-gwaje. Muna ganin cewa, suna da karancin kayayyakin kandagarki da karancin ma'aikatan aikin jiyya. Saboda haka, mun ba su horo da shawarwari don kara musu ilmin kandagarki da yadda za su kyautata tsarin kula da marasa lafiya."

Game da halin da kasar ke ciki na yakar COVID 19, masanan tawagar ba mai kawai sun samawa musu manufofi iri na kasar Sin, har ma sun ba da shawarwari bisa halin da suke ciki. Ban da wannan kuma, masanan sun tsai da takardar shawara kan kandagarkin cutar ga kasar, da kuma tambayoyi goma da amsa game da yakar cutar, don ba da shawara a bangare masana.

Zhu Yimin ya ce:

"Mataimakin ministan kiwo lafiya na kasar ya ce, kasar Sin ta fi samun nasara wajen yakar cutar. Manufofin da Sin take dauka sun fi ba da ma'ana a duniya, yana mai fatan wadannan manufofi za su kawo tasiri mai yakini ga kasar. Bayan tattaunawar da muka yi game da matsalolin da suke fuskanta, a ganinmu, kasar tana fuskantar matsaloli guda 10, game da matsalar fadakar da jama'a kan ilmin kandagarki da kiwon lafiya, mun yanke shawarar daukar bidiyo, wadanda za a gabatar da su ta telibijin kasar a nan gaba."

A sa'i daya kuma, ayyukan da tawagar ta yi sun samu amincewa daga kasar ta Equatorial Guinea. Firaministan kasar Francisco Pascual Obama Asue ya yabawa tawagar, yana mai cewa, ta kawowa kasar haske wajen magance cutar a kasar. Ya ce:

"Muna ganin cewa, Sin sahihiyar abokiya ce, abun dogaro. Sin ta riga ta samarwa kasashe fiye da 150 da kuma wasu kungiyoyin kasa da kasa taimakon gaggawa, da kuma turawa kasashe fiye da 20 tawagogin masananta, sannan kuma ta kira taro ta kafar bidiyo da kasashe ko yankuna fiye da 170, don gabatar da fasahohi da dabarunta ba tare da boye-boye ba. Kasar Sin ta hada gwiwa da kasa da kasa wajen yakar COVID-19 ne bisa dogaro da tunanin hadin kai da ra'ayin sadaukar da kai domin ci gaban wasu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China