Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikayyar dake tsakanin Sin da Afirka tana cin gajiyar ci gaban harkokin kasuwanci ta yanar gizo
2020-06-17 12:30:27        cri

Sakamakon saukin cinikayyar da ke tsakanin Sin da Afirka, harkokin kasuwanci ta yanar gizo sun samar da sabuwar dama ga hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuskar cinikayya.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, dandalin harkokin kasuwanci ta yanar gizo, sun samar da wani sabon zabi mai sauki ga masu sayayya na Afirka, wadanda suka samu ci gaba cikin sauri sosai. Kwararru sun nuna cewa, ana iya samun dimbin masu amfani da yanar gizo a Afirka, don haka akwai babbar kasuwa a fannin cinikayyar yanar gizo. Kuma kasar Sin na da fasahohi a fannonin raya harkokin cinikayya ta yanar gizo, da biyan kudi ta yanar gizo, da ma rarraba kayayyaki, lamarin da zai taimaka wa kasashen Afirka wajen kafa tsarin harkokin kasuwanci ta yanar gizo. A nan gaba kuma, cinikayyar dake tsakanin Sin da Afirka za ta ci gajiyar ci gaban harkokin kasuwanci ta yanar gizo, da ma cimma muradu da samun nasara tare.

"Gahawa na kasar Habasha, man shanu na kasar Mali, farin barkono na kasar Kamaru, gyada ta kasar Senegal da dai sauransu, ana sa ran ganin karin kayayyaki masu inganci da Afirka ke samarwa, za su shiga kasuwar kasar Sin ta harkokin kasuwancin yanar gizo." Mataimakiyar babban sakataren MDD, kuma Sakatariya mai zartaswa ta kwamitin kula da tattalin arzikin Afirka Madam Vera Songwe, ta yi wannan tsokaci ne bayan da ta shiga harkar sayar da kayayyaki ta hanyar daukar bidiyo kai tsaye a dandalin kasuwanci ta yanar gizo a kwanakin baya. Cikin wasu dakiku kalilan, an sayar da dukkan jakukuna 3000 na gahawa da Ruwanda ta samar, manoman Ruwanda kuwa sun yi ihu, sun yi murna da ganin hakan ta wayar salula. Ban da wannan kuma, Madam Songwe ta furta cewa, tattalin arziki ta yanar gizo na taka muhimmiyar rawa a kasar Sin, wanda zai taimaka wa 'yan kasuwa da manoma na Afirka wajen fita daga talauci. An ce, yawan kayayyakin da aka sayar a wannan karo ta hanyar daukar bidiyon kai tsaye, ya yi daidai da na wadanda aka sayar a duk shekarar bara.

Ruwanda kasa ce ta farko da ta kafa dandalin kasuwanci ta yanar gizo mai suna eWTP a duk nahiyar Afirka, wanda rukunin Alibaba ya taimaka wa kamfanoni matsakaita da kanana na duk duniya, wajen raya harkokin cinikayya ta yanar gizo. A shekarar 2019, a kan dandalin Alibaba, jimillar kudin da aka samu ta hanyar sayar da kayayyakin Ruwanda ta karu da kashi 124 bisa dari, yayin da jimillar kudin da aka samu ta hanyar sayar da kayayyaki zuwa ga Ruwanda, ta karu da kusan kashi 80 cikin dari. A karshen shekarar bara, kasar Habasha ita ma ta shiga tsarin eWTP, bisa aniyar raya tattalin arziki ta hanyar ci gaban harkokin kasuwanci ta yanar gizo.

Sakamakon bullar cutar COVID-19, an kawo illa sosai ga harkokin kasuwanci na yau da kullum na wasu kasashen Afirka, amma aikin sayayya ta yanar gizo ya samu bunkasuwa. Dandalin Kilimall, da masu zuba jari na kasar Sin suka kafa ya riga ya zama dandalin kasuwanci ta yanar gizo mafi girma a gabashin Afirka, wanda ya jawo kamfanoni fiye da 1000.

Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin, an ce, idan an dauki kayayyakin rigakafin annoba kamar marufin hanci da baki a matsayin misali, to an gano cewa, jimillar kudin sayarwa ta watan Afrilu ta ninka sau 97 bisa na watan Fabrairu. An ce, karin masu sayayya na Afrika na zabar biyan kudin ta yanar gizo bisa tsarin da dandalin Kilimall ke da shi. Cikin sa'o'i 24 kacal, masu sayayya za su iya samun kayayyakin kasar Sin da ma sauran abincin wurin. Ban da sayar wa Afrika kayayyakin Sin, masu sayayya na kasar Sin su ma suna iya sayen kayayyakin Afirka kamar su furanni, barasa, waken koko, da ma gahawa a kan wannan dandali na Kilimall.

Yanzu akwai masu amfani da yanar gizo kimanin miliyan 465 a nahiyar Afirka, ana sa ran wannan adadi zai kai miliyan 495 a shekarar 2025. Bisa hasashen da shafin intanat na Statista ya yi, an ce, yawan kudin da Afirka za ta samu ta hanyar raya harkokin kasuwanci ta yanar gizo zai kai dala biliyan 18.42 a shekarar 2020, yayin da jimillar za ta kai dala biliyan 34.66 ya zuwa shekarar 2024, wato matsakaiciyar jimillar za ta karu da kaso 17 a ko wace shekara.

Yanzu haka kasashen Najeriya, Kenya, da ma Afrika ta Kudu, kasashen Afirka guda uku ne da suka fi samun saurin ci gaban harkokin kasuwanci ta yanar gizo. Kaso 40 na kamfanonin kasuwanci ta yanar gizo sun kafa hadkwatarsu a Najeriya, Kenya kuwa na da muhallin biyan kudi ta yanar gizo mafi ci gaba, yayin da Afirka ta Kudu ke da boyayyen karfi sosai na raya kasuwanci da ketare ta yanar gizo.

Dandalin kasuwanci ta yanar gizo na Jumia da aka kafa a Najeriya ya shafi kasashen Afirka fiye da 10. An ce, yanzu yawan masu amfani da dandalin ya kai miliyan 6.4, wanda ya karu da kaso 51 bisa na bara. Yawan kudin da aka biya bisa tsarin JumiaPay a watanni uku na farkon bana ya karu da kaso 77 bisa na makamancin lokacin bara. Jeremy Hodara, daya daga cikin masu kafa tsarin JumiaPay ya bayyana cewa, harkokin kasuwanci ta yanar gizo na Afirka na samun saurin bunkasuwa, saurin karuwar masu amfani da Intanat da ma wayar salula ya samar da babbar damar raya kasuwanci, masu sayayya na bin al'adar sayen kayayyaki ta yanar gizo sannu a hankali.

Jeremy Hodara ya kuma bayyana cewa, ana fatan amfani da fasahohin da Sin ta samu, wajen raya harkokin kasuwanci ta yanar gizo don kara samun ci gaba. Dandalin kasuwanci ta yanar gizo na Afirka na son inganta hadin gwiwa tare da Sin. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China