Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Mali: Taron koli na hadin kan Sin da Afrika wajen yakar COVID 19 na da babbar ma'ana
2020-06-19 16:20:28        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron koli na hadin kan Sin da Afrika wajen yakar COVID-19 a daren ran 17 ga wata, inda ya ba da jawabi mai taken "Hadin kai wajen tinkarar mawuyacin hali na yakar COVID-19". Game da wannn taro, jakadan Sin dake Mali Zhu Liying, ya shaidawa manema labarai cewa, ba ma kawai taron na musamman a wannan karo na da babbar ma'ana ga Sin da Afrika ba ne kadai, har ma ga duk fadin duniya.

Zhu Liying ya ce, jawabin da shugaba Xi ya gabatar a gun taro ya nanata manyan ayyukan da ya kamata a nace gare su, wato yakar cutar, da hadin kan Sin da Afrika, da kuma inganta cudanyar bangarori daban-daban, kana da kara sada zumuncin Sin da Afrika. Wannan jawabi ba ma kawai ya samar da tushen hadin kan Sin da Afrika wajen yakar cutar ba ne, har ma ya ba da misali ga sauran kasashe, da nahiyoyi ta fuskar hadin kai.

Ban da wannnan kuma, a cewarsa, jawabin shugaba Xi, ya samu karbuwa matuka daga kafofin yada labarai, da ma masu amfani da Intanet na Mali. Wasu sun nuna cewa, ra'ayin shugaba Xi na cike da hange nesa, wanda ya bayyana fifikon da Sin take da shi, a fannin tsare-tsare, da matakai, da kuma karfin gudanar da harkokin kan ta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China