Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Ethiopian Airlines ya taimaka sosai ga bikin baje-kolin kayayyaki na Canton
2020-06-22 13:57:47        cri

Bayan da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Habasha wato Ethiopian Airlines ya kaddamar da layinsa tsakanin Guangzhou da Addis Ababa a shekara ta 2003, kawo yanzu, kamfanin ya yi jigilar fasinjoji 'yan kasuwan Afirka masu tarin yawa zuwa Guangzhou, domin halartar bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa, wanda aka fi sani da suna Canton Fair a turance. A kwanan nan, a wajen wani taron manema labarai da aka shirya a Guangzhou, jami'an dake aiki a filin saukar jiragen sama na Baiyun dake birnin da wakilan kamfanin Ethiopian Airlines sun bayyana irin dadadden zumunci dake tsakaninsu.

Idan an tabo batun kasuwanci tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ba za a manta da kamfanin Ethiopian Airlines ba. Shekaru 17 da suka gabata, kamfanin ya fara aikinsa a babban filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Baiyun dake Guangzhou, wanda ya kasance kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Afirka na farko da ya gudanar da aiki a Guangzhou. Doucoure Abdoulaye, shi ne shugaban babbar kungiyar 'yan kasuwan Mali dake kasar Sin. Ya bayyana cewa, tun daga wancan lokaci, an kara samun 'yan kasuwan kasashen Afirka wadanda ke halartar bikin Canton Fair a kasar Sin. Mista Doucoure ya ce:

"Tun daga wancan lokacin ya zuwa yanzu, ana kara samun 'yan kasuwan Afirka da suke halartar Canton Fair a Guangzhou. Hadin-gwiwar kasuwanci tsakanin Sin da Afirka na dada taka muhimmiyar rawa, al'amarin da ya samar da alheri da moriya ga bangarorin biyu, da taimakawa ci gaban dangantakarsu sosai. Wannan ma abun alfahari ne ga nahiyar Afirka."

Madam Lin Keru, jami'a ce dake aiki na tsawon shekaru 30 a babban filin saukar jiragen saman Baiyun dake Guangzhou, wadda ta ganewa idanunta bunkasuwar harkokin sufurin jiragen sama tsakanin Guangzhou da kasashen Afirka. Madam Lin ta bayyana wasu muhimman canje-canjen da aka samu bayan da kamfanin Ethiopian Airlines ya kaddamar da layin zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Guangzhou da Afirka, inda ta ce:

"Kamfanin Ethiopian Airlines shi ne kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Afirka na farko wanda ya zo kasar Sin don gudanar da ayyuka. Zuwa karshen bara, akwai kamfanonin Afirka shida da suka bude ofishinsu a filin jiragen sama na Guangzhou. Kuma a shekara ta 2003, fasinjojin Afirka kimanin dubu 30 ne kawai, amma a shekarar da ta gabata, yawan fasinjojin Afirka ya zarce dubu 700. Kuma tun farkon farawa, jiragen sama biyu ne kadai na kamfanin Ethiopian Airlines suke zirga-zirga tsakanin Addis Ababa da Guangzhou, amma yanzu, wato kafin barkewar annobar COVID-19, adadin jiragen saman kamfanin da ya yi tafiye-tafiye tsakanin wuraren biyu, ciki har da na kaya da na fasinja, ya kai 19 a kowace rana."

Cutar mashako ta COVID-19 na ci gaba da bazuwa a duk fadin duniya, inda kamfanin Ethiopian Airlines ya taimaka matuka wajen jigilar kayayyakin yaki da cutar a duk fadin duniya. Daga watan Janairu zuwa Yunin bana, kamfanin ya yi amfani da jiragensa 503 domin shigowa gami da fitar da kayan yaki da cutar da yawansu ya zarce ton dubu 20 a kasar Sin. Kuma an yi bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa na Canton Fair na bana ta kafar sadarwar Intanet, sakamakon yaduwar cutar a duniya. A nasa bangaren, manajan kula da sayar da tikiti na kamfanin Ethiopian Airlines dake Guangzhou Mista Mehari Assefa ya bayyana cewa:

"Dadadden tarihi, da isassun kayayyaki, da halartar masu sayayya a gagarumin bikin Canton Fair duk sun burge mu kwarai da gaske. Muna da yakinin cewa, irin wannan biki zai kara samar da damammaki ga hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya. A halin yanzu muna fuskantar wani sabon kalubale, wato tasirin da cutar COVID-19 ke haifarwa. Ya kamata mu tsaya kafada da kafada da daukacin al'ummar kasar Sin, domin himmatuwa wajen dakile cutar. Za mu yi bakin kokarinmu domin tabbatar da ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Sin da Afirka."

A matsayin kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mafi girma a nahiyar Afirka, Ethiopian Airlines ya taba gamuwa da yaduwar cututtuka ciki har da SARS da Ebola da sauransu, kuma a yayin yaduwar cutar COVID-19 a bana, babu ma'aikacin jirgin ko daya da ya harbu da cutar, abun da ya aza tubali mai inganci ga zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Ana da yakinin cewa, bayan yaduwar cutar, kamfanin Ethiopian Airlines zai dauko karin fasinjojin Afirka don su halarci bikin Canton Fair a Guangzhou.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China