Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fannin sarrafa hajoji na Afirka na farfadowa
2020-06-26 10:16:12        cri

Wasu masu ruwa da tsaki a ayyukan masana'antu dake sarrafa hajoji a nahiyar Afirka, sun bayyana yadda fannin ke farfadowa sannu a hankali, sakamakon matakai masu tasiri da ake aiwatarwa, a bangaren yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Masu masana'antun kasashen Kenya, da Masar da na Zambia sun shaidawa kafafen watsa labarai hakan a jiya Alhamis.

Da yake tsokaci kan wannan batu, shugaban kungiyar masu masana'antun kasar Kenya Phyllis Wakiaga, ya ce an ga alamun farfadowar al'amura, yayin da gwamnati da sassa masu zaman kansu, suka fara sayen hajojin da ake sarrafawa a cikin gida.

Shi kuwa a nasa bangaren, shugaban kungiyar masu harkar fiton kaya dake Kenya Gilbert Langat, cewa ya yi yanzu haka masu masana'antu, na sayo kayan aiki na watanni 6 ne maimakon na watanni 3, wanda hakan ke haifar da karancin fili, ko wuraren sauke kayan a tashoshin jiragen ruwan kasar.

Langat ya ce barkewar cutar COVID-19 ya gwada bukatar dake akwai, ta kara inganta tsarin ba da hidima a fannin fiton kayayyaki a kasashen Afirka. Ya ce kasashen nahiyar na bukatar daga matsayin sashen ba da hidimominsu, ta yadda zai zamo mai inganci da arha, ga masu shige da ficen hajoji.

Daga nan sai ya buga misali da tashar jiragen ruwa ta Mombasa, da tashoshin tudu na birnin Nairobi da garin Naivasha, wadanda a cewarsa, idan za a samar musu da na'urorin zamani, hakan zai rage bukatar zirga zirgar jama'a ta kai tsaye, ya kuma inganta salon gudanar da ayyuka a cikinsu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China