Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IOM: an ceto bakin haure 71 daga gabar ruwan Libya
2020-06-26 10:41:07        cri
Hukumar kula da kaura ta duniya IOM, ta ce an ceto bakin haure 71 daga gabar ruwan Libya, cikinsu har da mata da yara.

Bisa wani sako da IOM ta wallafa a shafinta na Tweeter, tuni a ranar Laraba da daddare, jami'an tsaron ruwan Libya suka kwashe bakin hauren 71 da suka hada da mata 4 da yara 2, zuwa birnin Tripoli.

Tun bayan hambarar da mulkin Muammar Gaddafi a shekarar 2011 da barkewar rikici da rashin tsaro, Libya ta zama hanyar da dubban bakin haure suka zaba son tsallaka tekun Bahar Rum zuwa Turai.

Kafin hukumomin Libya su rufe iyakokin kasar a kokarin yaki da cutar COVID-19, IOM na gudanar da wani shirin mayar da bakin hauren da suka zabi komawa gida, wanda ke shirya komawar bakin hauren dake watangarari a Libya zuwa kasarsu ta asali.

Hukumar IOM ta ce, yayin da har yanzu ba a bude hanyoyin sufurin jiragen sama saboda COVID-19 ba, sama da bakin haure 1,000 dake watangarari a Libya, sun yi rejista da shirin domin komawa gida su sadu da iyalansu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China