Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaba da aiwatar da matakan kulle saboda COVID-19 na kara ta'azzara kalubalen tattalin arziki da zamantakewa a Afrika
2020-06-30 09:57:24        cri

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Afrika, (Africa CDC), ta ce matakan kulle da ake ci gaba da aiwatarwa na kara ta'azzara kalubalen tattalin arziki da zamantakewa da lafiyar kwakwalwa da kuma lafiyar al'umma a nahiyar.

Sabon rahoton da hukumar ta fitar mai taken "ka'idojin sassauta kulle: duba yiwuwar sassauta matakan da aka dauka kan zamantakewa da lafiyar al'umma a kasashe mambobin AU" ya jaddada mummunan tasirin matakan kulle da aka dauka saboda COVID-19.

Rahoton wanda ya yi tantamar gaggawar aiwatar da matakan kulle da kasashen Afrika suka yi, ya samar da lokacin tsarawa da shirya ayyukan kiwon lafiya da inganta karfin gwaji, ya bayyana wasu daga cikin illolin da za su yi ga tsarin lafiyar al'umma da zamantakewa, bisa la'akari da yanayin bangarorin a fadin nahiyar.

Cibiyar Africa CDC ta kuma ba da misali da hasashen asusun ba da lamuni na duniya, wanda ya ce a bana, za a samu karin mutane miliyan 84 zuwa 132 da za su shiga cikin matsananciyar fatara, inda za a samu karuwar adadin da kaso 40 zuwa 50 a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China