Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nigeriya za ta dage dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin kasar
2020-06-30 14:29:36        cri

Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta dage dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin kasar, bayan shafe makonni da dama tana aiwatar da matakan dakile annobar COVID-19, wadda ta harbi mutane sama da 25,000 a kasar.

Matakin wanda ya samu amincewar shugaban kasar Muhammadu Buhari, na zuwa ne yayin da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar NCDC, ta tabbatar da yammacin jiya cewa, an samun sabbin mutane 566 da suka harbu da cutar a jihohin kasar 19 da birnin tarayya Abuja, wanda ya kawo adadin masu cutar a Nijeriya zuwa 25,133, inda mutane 573 suka mutu, sannan 9,402 suka warke.

Sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha, ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, za a fara zirga-zirga tsakanin jihohin kasar ne daga gobe Laraba, amma dokar takaita zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa 4 na safiya, za ta ci gaba da kasancewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China