Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: Ya kamata kasar Amurka ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan Sin
2020-07-01 19:42:27        cri
A yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ja hankalin kasar Amurka, da ta daina yin shisshigi cikin harkokin gidan kasar Sin, ta hanyar yin amfani da batun yankin Hong Kong.

Kafin hakan, wasu 'yan siyasan kasar Amurka da suka hada da shugabar majalissar wakilan kasar Nancy Pelosi, da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, da dai sauransu, sun bayyana ra'ayinsu na kin amincewa da kafurwar dokar tsaron kasa, wadda ta shafi yankin Hong Kong na kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China