Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta mayar da martani ga matakan kasar Amurka na kayyade harkokin kafofin watsa labaru na kasar Sin
2020-07-01 20:00:27        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya furta a yau Laraba cewa, za a dauki wasu matakai kan wasu kafofin watsa labaru guda 4 na kasar Amurka, a matsayin mai da martani ga matakan da kasar Amurka ta dauka, na kayyade harkokin kafofin watsa labaru na kasar Sin.

Matakin ya shafi kamfanonin AP, da UPI, da CBS, gami NPR na kasar Amurka, inda aka bukace su da su samar da rubutattun bayanai, game da ma'aikatansu a cikin kasar Sin, da harkar kudi, da yadda ake gudanar da harkokinsu, gami da kadarorin da suka mallaka, da dai makamantansu, cikin kwanaki 7.

A cewar Zhao, kasar Sin ta tsai da manufar ne don kare kanta, sa'an nan ya bukaci kasar Amurka da ta daina yin tarnaki ga harkokin kafofin watsa labaru na kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China