Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dokar tsaron kasa ta Hongkong ba za ta lahanta ikon alkalai wajen yanke hukunci ba
2020-07-01 20:53:12        cri

A jiya Talata ne aka aiwatar da dokar ba da tabbaci ga tsaron kasar Sin ta yankin musamman na Hongkong, inda dokar ta yi tanadin cewa, kantomar yankin za ta nada alkalai, don su daidaita batun aikata laifin kawo barzana ga tsaron kasar Sin.

Darektan kwamiti mai kula da shari'a da doka na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Shen Chunyao, ya bayyana a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, wannan doka ba za ta kawo ko wane mummunan tasiri, ga ikon yanke hukunci na alkalai a kotun Hongkong ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China