Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya zai ba da rancen kudin dala biliyan 50 ga yankin kudu da Sahara a 2020
2020-07-02 09:36:38        cri

A ranar Laraba bankin duniya ya sanar cewa, zai bayar da rancen kudin shillings na kasar Kenya tiriliyan 5.3, kwatankwacin dala biliyan 50 ga kasashe 48 dake shiyyar kudu da hamadar Sahara ta Afrika a cikin wannan shekara.

Bankin ya ce, rancen kudin da zai bayar ya yi yawa, kuma adadin ya kai kashi daya bisa uku na jimillar rancen kudin da bankin zai bayar a wannan karo.

A sanarwar da bankin ya fitar, ya ce, wannan adadin kudin ya kusa ninka adadin kudin da shiyyar ta karba rance a shekaru goman da suka wuce.

Muhimman ayyukan bankin duniyar sun hada da fannin aikin noma, kasuwanci da sufuri, makamashi, ilmi, kiwon lafiya da samar da ruwan sha da tsaftar muhalli.

Bankin ya ce ayyukan da zai gudanar a yankin kudu da hamadar Saharar Afrika a yanzu, za su kasance karkashin kulawar mataimakan shugabanni biyu dake lura da shiyyar yammaci da tsakiya, da kuma gabashi da kudancin Afrika.

Bankin duniya ya sanar da matakin da ya dauka a farkon shekarar 2020, wanda ya fara aiki tun daga jiya ranar Laraba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China