Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe 46 sun goyi bayan matakan kasar Sin na yaki da taaddanci da tsattsauran raayi a Xinjiang
2020-07-02 09:48:45        cri

Kasar Belarus ta gabatar da wata sanarwar hadin gwiwa a madadin kasashe 46 a jiya Laraba, yayin zaman taro na 44 na hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD, inda suka bayyana goyon bayansu kan matakan yaki da ta'addanci da kawar da tsattsuran ra'ayi da Sin take dauka a yankin Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa.

Sanarwar ta kuma yi kira da a daina zargin kasar Sin ba tare da kwararan shaidu ba. Sun kuma nanata cewa, ya kamata hukumar ta rika gudanar da ayyukanta ba tare da wata rufa-rufa ba, ko nuna son kai, ko fito na fito ba kuma tare da sanya batu na siyasa ba.

Har ila sanarwar ta bayyana kudurin kasashen, na yayata da kare hakkin dan-Adam da nuna adawa da yadda ake siyasantar da batutuwan da suka shafi kare hakkin dan-Adam da nuna fuska biyu.

Kasashen sun kuma yaba da jerin matakan da kasar ta dauka, don mayar da martani kan wannan barazana kamar yadda doka ta tanada, wajen kare hakkin dukkan kungiyoyin kabilun dake jihar Xinjiang. Suna masu cewa, a cikin shekaru uku a jere, ba a kai harin ta'addain koda sau daya a jihar ba. Abin da ke alamta cewa, an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Xinjiang.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China