Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyun siyasa 100 na duniya sun taya murnar kafuwar JKS shekaru 99
2020-07-02 10:33:39        cri

Sama da jam'iyyun siyasa 100 na kasashen duniya sun taya babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS Xi Jinping murnar cika shekaru 99 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda ya fado a ranar Laraba, inda suka yaba da irin dimbin tarihin da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta kafa, da kuma manyan nasarorin da kasar ta cimma.

A sakon da suka aika kwanan nan zuwa ga sashen hulda da kasa da kasa na kwamitin tsakiyar JKS, jami'iyyun siyasar sun ce, sun yi amanna cewa kasar Sin dake karkashin jagorancin jam'iyyar JKS, babu tantama za ta kai ga matsayi mai haske a nan gaba, kana za ta bayar da babbar gudunmawa ga ci gaban dukkan bil Adama.

Jam'iyyar kwaminis ta kasar Masar ECP, ta ce, a shekaru 99 masu daraja da suka gabata, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta jagoranci al'ummar Sinawa wajen cimma muhimman nasarori ta fuskar bunkasuwar al'amurran siyasa, tattalin arziki, zaman rayuwar al'umma, da sauran fannoni, kana sun bayar da gagarumar gudunmawa ga yunkurin da duniya ke yi a yaki da mulkin danniya, da mulkin mallaka, da kuma tabbatar da adalci a duniya.

Ita ma jam'iyyar ANC mai mulkin Afrika ta kudu ta ce, kafuwar jam'iyyar JKS tana da matukar muhimmanci ga tarihin Sinawa da daukacin mutanen duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China