Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kila annobar COVID-19 za ta sake barkewa sakamakon dakatar da matakan dakile da kandagarkin annobar
2020-07-02 10:41:35        cri

Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban darektan hukumar lafiya ta duniya wato WHO ya bayyana jiya Laraba cewa, hanya mafi dacewa ta yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ita ce daukar matakai daga dukkan fannoni, ciki had da gano wadanda suka kamu da cutar, da killace su, yi musu gwaji da ba su magani, gano da killace dukkan wadanda suka yi mu'amala da masu fama da cutar, horas da ma'aikatan lafiya da ba su kayayyakin aiki, karfafa gwiwar daukacin al'umma na daukar matakai da dai sauransu.

A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa, babban darektan ya kara da cewa, yanzu haka wasu kasashe sun fara dakatar da matakan dakile da kandagarkin annobar. Ana hasashen cewa, kila annobar za ta sake barkewa a wasu kasashe. Amma kasashen da suka dauki matakai daga dukkan fannoni za su samu nasarar yaki da annobar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China