Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin: Kudurin da kwamitin sulhu ya cimma kan COVID-19 nasara ce ga alakar kasa da kasa
2020-07-02 10:50:22        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana cewa kudurin da kwamitin sulhun MDD ya amince da shi kan COVID-19, nasara ce ga kasancewar bangarori daban-daban.

Wakilin na kasar Sin ya bayyana haka ne, bayan kada kuri'arsa, yana mai cewa a wannan lokaci mai sarkakiya da duniya ke na yaki da cutar COVID-19, nauyi ne dake kan kwamitin sulhun na daukar matakan da suka dace don rage tasirin cutar kan zaman lafiya da tsaron duniya.

Amincewa da kudirin mai lamba 2532, ya nuna karfi da jagorancin kwamitin na daukar matakin da ya dace, abin da ke nuna nasarar hakan ga alakar kasashen duniya.

Ya ce, koda yake kudirin ya dan gamu da turjuya, ganin yadda wata mambar kwamitin ta tsaya kai da fata na ganin an dauki matsaya guda, inda ta canja magana da ma karya alkawarin da ta yi, da yin watsi da kiraye-kirayen kasashen duniya. Abin da ya sa aka rika samun jinkirin tattaunawa.

Zhang Jun ya ce, da farko, kasar Sin tana goyon bayan kiran da babban sakataren majalisar ya yi na neman tsagaita bude wuta a duniya da shirin MDD na samar da jin kai a duniya, matakan da dukkansu suka samu sahalewar kudirin.

Shi dai kudirin mai lamba 2532 wanda ya samu goyon bayan baki dayan mambobin kwamitin 15, ya bukaci da a tsagaita bude wuta baki daya kamar yadda kwamitin ya zayyana cikin ajandarsa. Ya kuma yi kira ga dukkan kungoyoyi masu dauke da makamai dake gwabza fada, da su hanzarta dakatar da fada na a kalla kwanaki 90 a jere, ta yadda za a samu damar kai taimakon jin kai, da hidimomin da suka dace da kwashe masu bukatar kulawar lafiya.

Kasar Sin tana kira ga kasashen duniya, da su yi amfani da wannan dama, wajen karfafawa bangarorin dake fada da juna gwiwar amsa kiran da babban sakataren MDD ya yi, na hanzarta dakatar da tashe-tashen hankula, da yin aiki tare don yakar COVID-19, da kare rayuka, da himmatuwa ga sasanta rikice-rikice cikin lumana, da tabbatar da kai taimakon jin kai da inganta matakan tsaro da kare lafiyar ma'aikatan dake aikin wanzar da zaman lafiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China