Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan hasarorin da aka samu kan sha'anin yawon shakatawa na duniya a sakamakon cutar COVID-19 ya kai dala biliyan 1200
2020-07-02 11:13:27        cri
Kungiyar cinikayya da bunkasuwa ta MDD ta gabatar da rahoto a jiya,inda ta ke cewa, a sakamakon cutar COVID-19, an dakatar da harkokin sha'anin yawon shakatawa a duniya har tsawon watanni 4, kuma hasarar da fannin ya tafka, ta kai dala biliyan 1200, wanda ya yi daidai da kashi 1.5 cikin dari na yawan GDP na duniya.

Rahoton ya yi nuni da cewa, koma bayan da bangaren yawon shakatawa ya samu, za ta kara kawo illa ga tattalin arzikin kasashe masu tasowa. Kungiyar ya yi hasashe cewa, koda ana cikin yanayi mai kyau, a sakamakon koma bayan da yawon shakatawa ya fuskanta, ya sa alkaluman GDP na kasar Jamaica zai ragu da kashi 11 cikin dari, yayin da na kasar Thailand zai ragu da kashi 9 cikin dari. Kana yawan GDP na kasashen Kenya, da Masar, da Malaysia da sauransu zai ragu da fiye da kashi 3 cikin dari. Hakazalika, kasuwar yawon shakatawa ta kasashe masu ci gaba da dama, ciki har da Faransa, da Girka, da Italiya, da Portugal, da Spaniya, da Amurka da sauransu, za su fuskanci koma baya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China