Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun tallafa wa juna ya taimaka wajen fitar da masu fama da talauci daga kangin da suke ciki
2020-07-02 18:25:35        cri

Birnin Fuyuan da ke lardin Heilongjiang na kasar Sin yana bangare da ya fi gabashi na kasar Sin, wanda kuma yake makwabtaka da kasar Rasha. Don haka, a 'yan shekarun da suka wuce, an gina yankin ciniki a tsakanin al'ummun kasashen biyu mazauna wurin, tare kuma da kafa asusun tallafawa juna, asusun da masu sayen kayayyaki suke zuba wani kaso na kudin da suka biya wajen sayen kaya, don tallafa wa masu fama da talauci na wurin.

Akasarin masu fama da talauci a birnin na Fuyuan sun fada cikin kangin talauci ne a sakamakon ciwo ko nakasa da suka same su. Don haka, tun daga shekarar 2016, an kafa asusun a birnin, a wani yunkuri na tallafa wa masu karamin karfi bisa masu karfi. Asusun da aka zuba kudin da aka samu daga harkokin ciniki da yawon shakatawa zuwa kauyuka da sauransu a ciki, don a sake raba kudin da aka samu, ta yadda masu karamin karfi ma za su iya morewa. Kudin da aka zuba cikin asusun daga bangaren ciniki a tsakanin al'ummun kasashen biyu mazauna wurin ya riga ya kai yuan sama da miliyan uku. (Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China