Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba za a cimma nasarar shafawa kasar Sin bakin fenti ta fakewa da batun Xinjiang ba
2020-07-02 19:45:13        cri

Yau Laraba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce, kasashe 46 sun nanata matsayin da suke kai, na goyon bayan matakin da Sin take dauka a jihar Xinjiang, yayin taron kwamitin kare hakkin Bil Adama na MDD. Ya kuma ce wasu kasashen yamma dake adawa da Sin, ba za su cimma nasarar shafawa kasar ta Sin bakin fenti, ta hanyar fakewa da batun Xinjiang ba.

Zhao Lijiang ya nanata cewa, Sin na yin iyakacin kokarin hadin kai da bangarori daban-daban, don ingiza tsarin kare hakkin bil Adama tsakanin bangarori daban-daban, da kuma nacewa ga muradu, da ka'idojin mulkin MDD, don daidaita batun hakkin bil Adam cikin adalci da daidaito, har ma da raya wannan sha'ani yadda ya kamata, bisa hadin kai da gudanar da shawarwari a duniya.

Bugu da kari, jami'in ya ce, Sin ba za ta amince ta tsoma baki cikin harkokin sauran kasashe, ta fakewa da batun hakkin Bil Adama ba, kuma tana kalubalantar kasashe da wannan batu ya shafa, da su yi watsi da siyasantar da wasu harkoki, da yin fuska biyu, su kuma daina shisshigi cikin harkokin sauran kasashe da sunan kare hakkin Bil Adama. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China