Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta nuna takaici kan yadda Amurka ta zartas da dokar da ta shafi Hong Kong na Sin
2020-07-02 20:17:18        cri
Dangane da dokar "cin gashin kai a yankin Hong Kong", wadda majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijiang, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin ta nuna matukar rashin jin dadi da kin amincewa da matakin na Amurka, bisa wannan dokar da za ta yi illa ga batun yankin Hong Kong na kasar Sin.

Zhao ya kara da cewa, harkokin Hong Kong, ciki har da batun kafuwar dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin na Hong Kong, wasu ayyuka ne na cikin gidan kasar Sin, don haka wata kasar waje, ba ta da hurumin tsoma baki ciki. Ya ce yunkurin kasar Amurka na neman hana kasar Sin aiwatar da dokar tsaron kasa da ta shafi Hong Kong ba zai yi nasara ba.

A nasa bangare, kwamiti mai kula da harkokin waje, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, shi ma ya ba da wata sanarwa a yau Alhamis, inda ya yi Allah wadai, da mummunar dokar da kasar Amurka ta zartas. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China