Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aikin dake gaban kiyaye tsaron kasar dake shafar yankin Hongkong shi ne aiwatar da harkokin yankin bisa doka
2020-07-02 21:41:46        cri

Ayyukan dake gaban bunkasuwar yankin Hongkong su ne tsaron kasar, da kwanciyar hankalin al'umma, da tsarin gudanar da harkoki bisa doka da shari'a. Kafin zartas da dokar tsaron kasa dake shafar yankin Hongkong, an gaza samun irin wannan doka, hakan ya sa ba a iya gurfar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu.

Zartas da wannan doka cikin lokaci ya farantawa jama'a rai. Saboda dokar ta biya bukatun yawancin jama'ar yankin Hongkong, inda ta samar da tabbaci ga tsaron kasa dake shafar yankin Hongkong, da tsaron al'umma, da kuma tsaron daidaikun mutane bisa tushen tsarin "kasa daya kasancewar tsarin mulki iri biyu", har ma ta aza tubali mai inganci ga tushen gudanar da harkokin yankin bisa doka.

Tabbatar da tsaron kasa aiki ne mai tushe, wajen tabbatar da tsaron yankin Hongkong da ma jama'arsa, kuma dokar ta zama mataki mai inganci na tabbatar da bunkasuwar yankin Hongkong a duk fannoni.

Mun yi imani cewa, Hongkong zai iya samun sabuwar bunkasuwa, bisa goyon bayan kwamitin tsakiya da jama'ar kasar baki daya, ciki hadda mazauna yankin na Hongkong. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China