Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samar wa Sudan ta kudu tallafin kayayyakin yaki da COVID-19
2020-07-03 09:52:48        cri

Ofishin jakadancin kasar Sin a Sudan ta kudu da kungiyar tallafawa al'umma ta Sudan ta kudu karkashin jagorancin mai dakin shugaban kasar Mary Ayen Mayardit sun shirya bikin mika tallafin kayayyakin yaki da annobar COVID-19 ga gwamnatin Sudan ta kudu a jiya Alhamis.

Hua Ning, jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu ya ce, yayin da ake fuskantar kalubalolin annobar COVID-19, kasar Sin da Sudan ta kudu suna yin hadin gwiwa domin yaki da cutar da kuma kokarin kawar da wahalhalun da ake fuskanta tare.

Kwanan baya, farfesa Peng Liyuan, mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta amsa bukatar da kungiyar raya ci gaba ta matan shugabannin kasashen Afrika, ofishin jakadancin Sin ya sanar da hakan cikin bayannin da ya wallafa a shafinsa na intanet.

Mayen Machut Achiek, mataimakin sakataren ma'aikatar lafiyar Sudan ta kudu ya godewa gwamnatin kasar Sin sakamakon samar da gudunmawar kayayyakin kiwon lafiya ga kasar.

Ya ce gwamnatin Sin da jama'arta sun bayar da muhimmiyar gudunmawa ga Sudan ta kudu don yaki da cutar COVID-19, wanda hakan wata muhimmiyar alama ce dake kara bayyana kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China